Kano: Shugaban masu rinjayen majalisar wakilai ya yi tsokaci a kan mace-mace
Alhassan Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, ya ce akwai yuwuwar mace-macen da ake yi a jihar Kano ya wuce rayukan da mayakan Boko Haram suka dauka a kasar nan, matukar ba a dauka mataki ba.
Doguwa, mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada a majalisar wakilai, ya sanar da hakan ne a taron zauren majalisar na yau Talata yayin da yake mika bukatar kawo karshen mace-mace a jiharsa.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, ana ta mace-mace a jihar Kano wacce ake dangantawa da annobar COVID-19.
Dan majalisar ya ce daga abinda ke faruwa a jihar Kano, lamarin ba na tashin hankali bane, har da alhini.
Ya ce akwai bukatar aikin gaggawa don ceto jihar. Akwai bukatar 'yan majalisar su gaggauta kawo karshen mace-macen tare da dakile hakan daga zuwa wani wuri.
"Ina tsoron yadda lamurra ke tafiya a jihar Kano. Idan ba a dauka mataki ba, akwai yuwuwar barnar da za ta faru ta fi ta Boko Haram muni," yace.

Asali: Twitter
KU KARANTA: COVID-19: Martanin jama'ar jihar Kano a kan hukuncin Buhari
"Boko Haram na kisa ne ta hanyar amfani da bindiga da fushi. Wannan kuwa na kashe jama'a ne a hankali ta hanyar wawurewa da rage yawansu.
"Ballantana a tsakiyar birnin Kano inda akwai a kalla akwatunan zabe 600. Mutanen nan na dankare ne a wuri daya ba tare da wani rarrabewa ba." yace.
Shugaban majalisar ya kara da cewa wannan ba abu bako bane a jihar ballantana a yayin lokacin rani. Amma wannan na da matukar firgitarwa.
"A baya, mun saba samun irin wannan mace-macen ne a yayin rani amma abinda muke gani yanzu ya fi karfin hankali," yace.
A ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin garkame jihar na makonni biyu yayin da ake bincikar sanadin mace-macen.
Kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana, zai gaggauta daukan matakai don shawo kan matsalar da jihar ta Kano ke ciki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng