Mace ta farko da ta fara zama Kwamandar Hisbah a Kano ta rasu

Mace ta farko da ta fara zama Kwamandar Hisbah a Kano ta rasu

Allah ya yi wa Halima Shittu, daya daga cikin kwamandojin Hisbah na farko rasuwa a Kano a ranar Litinin kamar yadda wani na kusa da iyalan ta ya sanar.

The Nation ta ruwaito cewa Halima Shittu ta rasu ne tana da shekaru 55 a duniya.

Maimuna Shitu, daya daga cikin yan uwan mamaciyar ta shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, a ranar Talata cewa ta rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a Kano.

Mace ta farko da ta fara zama Kwamandar Hisbah a Kano ta rasu

Mace ta farko da ta fara zama Kwamandar Hisbah a Kano ta rasu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Covid-19: Yara biyu sun mutu a dandazon jama'a yayin siyayyar azumin Ramadan

Ta ce, "Ta rasu ba bar mijinta, fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Abdulwahab Abdullahi da yara shida.

"Babban dan ta, Malam Abdullahi Abdulwahab ma'aikaci ne a Jamiar Bayero ta Kano."

Halima Shittu ta bayar da gagarumin gudunmawa wurin cigaban Hukumar Hisbah a Kano.

Ta taimaka wurin samar da guraben karo karatu ga mata a Najeriya da Afirka baki daya a matsayin ta na shugaban Kungiyar Mata Musulmi na Africa, AMEWA.

Marigayiyar ta sha fitowa a shirye shiryen rediyo ta talabijin da ke gudanarwa domin koyar da mutane ilimin addinin musulunci musamman lokacin azumin watan Ramadana kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel