Coronavirus za ta yi sanadiyyar mata miliyan 7 su dauki ciki – Majalisar dinkin duniya

Coronavirus za ta yi sanadiyyar mata miliyan 7 su dauki ciki – Majalisar dinkin duniya

Hukumar majalisar dinkin duniya dake kula da yawan al’ummar duniya, UNFPA, ta bayyana cewa za’a samu juna biyu da ba’a shirya daukan su ba guda miliyan bakwai a duk fadin duniya.

BBC Hausa ta bayyana hukumar UNFPA ta bayyana haka ne a ranar Talata yayin da take sanar da hasashen da ta yi game da halin da za’a iya shiga a dalilin dokar hana fita saboda Coronavirus.

KU KARANTA: Wata Iska mai karfin gaske ta kashe mutane 2 a Taraba, ta lalata gidaje 500

UNFPA ta ce idan aka kara wata 6 a dokar hana fita, za’a samu kimanin mata miliyan 47 a kasashe masu tasowa da ba zasu iya samun hanyoyin da suke bi wajen hana daukan ciki ba.

Saboda haka UNFPA ta tabbatar da cewa sakamakon binciken da ta yi ya nuna mata fiye da miliyan 7 za su iya samun juna biyu sakamakon halin kulle da rashin fita da ake ciki.

Coronavirus za ta yi sanadiyyar mata miliyan 7 su dauki ciki – Majalisar dinkin duniya
Coronavirus za ta yi sanadiyyar mata miliyan 7 su dauki ciki – Majalisar dinkin duniya
Asali: Depositphotos

Haka zalika baya ga miliyoyin juna biyu da hukumar UNFPA take hasashen za’a samu a wannan lokaci, za kuma a samu hauhawar rikice rikice tsakanin ma’aurata a wannnan lokaci.

“Za’a samu karuwar rikici tsakanin ma’aurata fiye da miliyan 30 a wannan lokaci.” Inji UNFPA.

A wani labarin kuma, Fiye da mutane 700 sun mutu bayan sun kwankwadi barasa a matsayin maganin annobar Coronavirus a kasar Iran, domin a tunaninsu giya tana maganin cutar.

Aljazeera ta ruwaito hukumar yaki da Coronavirus a kasar Iran ce ta bayyana haka, inda tace mutane 728 ne suka mutu daga watan 20 ga watan Feburairu zuwa 17 ga watan Afrilu.

Gwamnatin Iran ta ce an samu karuwar mace mace daga shan barasa ninki 10 a shekarar daya data gabata, inda a shekarar 2019 aka samu mutane 66 da suka mutu sakamakon shan giya.

Kakaakin ma’aikatar kiwon lafiya na Iran, Kianoush Jahanpour ya ce mutane 5,011 ne suka sha guba a garin shan Methanol dake cikin giya, mutane 90 sun rasa idanunsu a dalilin haka.

Kasar Iran ita ce kan gaba a yankin gabas ta tsakiya wajen samun mace macen mutane a dalilin Coronavirus, inda mutane 5,086 suka mutu, yayin da ta kama wasu 91,000.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel