COVID-19: Dakin gwajin jihar Kano ya dawo aiki

COVID-19: Dakin gwajin jihar Kano ya dawo aiki

Darakta janar din hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC, Dr Chikwe Ihekweazu, ya bayyana cewa dakin gwajin kwayar cutar Covid-19 na jihar Kano zai ci gaba da aiki a yau Talata.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, cibiyar kwaya daya tak da ke asbitin koyarwa na Malam Aminu Kano ta dakata da aiki bayan karewar kayan aikinsu.

Ihekweazu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja a yayin bayani ga kwamitin fadar shugaban kasa na yakar cutar Covid-19.

Kamar yadda yace, NCDC ta mayar da hankali wajen yakar muguwar annobar da ta addabi kasar nan.

"Ina so in tunatar da kowa cewa mun mayar da hankali a kan abinda muke son cimma wa. Kara yawan dakunan gwajin kwayar cutar a kasar nan zai taka rawar gani wajen shawo kanta.

"Kowa ya san yawan jama'ar jihar Kano. Yawan jama'ar da ke kamuwa da cutar a jihar Kano ya zama abun mamaki.

"Tun bayan bayyanar cutar a mutum na farko a makonni biyu da suka gabata, Kano ta ci gaba da zama inda hankulanmu suka karkata har zuwa tsayawar aikin dakin gwajin.

"A halin yanzu, jihar Kano ce ta uku a fadin Najeriya a masu yawan cutar. Akwai tabbatattun masu cutar har 77 a cikin mutum 1,273 da muke da su a Najeriya," yace.

COVID-19: Dakin gwajin jihar Kano ya dawo aiki
COVID-19: Dakin gwajin jihar Kano ya dawo aiki
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa SGF Boss Mustapha, ministan lafiya da shugaban NCDC kiran gaggawa

Ihekweazu ya ce NCDC na kokarin bincikar sila ko kuma tushen mace-macen da jihar kano ke fuskanta a cikin kwanakin nan.

Ya ce cibiyar na yin duk abinda ya dace don ganin cewa dakin gwajin na jihar Kano ya ci gaba da aiki.

Shugaban hukumar NCDC din ya ce dakin gwajin ne ke bai wa samfurin jinin wadanda ake zargi a jihohin Arewacin kasar nan masauki.

"Ina farin cikin sanar da ku cewa dakin gwajin jihar Kano zai ci gaba da aiki. Za a ci gaba da gwada samfur kamar yadda ya fara.

"Ba karamin kokari muka yi ba kuma aikin ya bukaci hankulan dukkan kungiyarmu. Ma'aikatan dakin gwajin na jihar Kano da kuma wasu mutane sun matukar taimakawa.

"Ba za mu dakata ba har sai dakin gwajin ya ci gaba da aiki yadda ya dace," yace.

Ya kara da cewa al'amuran da suke faruwa a jihar Kano sun yi yawa kuma ana kokarin shawo kan matsalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel