Gwamnatin Tarayya ta gargadi gwamnoni a kan gasar adadin masu cutar korona a jihohinsu

Gwamnatin Tarayya ta gargadi gwamnoni a kan gasar adadin masu cutar korona a jihohinsu

Gwamnatin tarayya ta zargi gwamnonin Najeriya da yin gasa a tsakaninsu ta fuskar adadin masu dauke da kwayoyin cutar coronavirus a jihohinsu.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, wannan lafazi ya fito ne daga bakin babban jami'i na kwamitin kar ta kwana da fadar shugaban kasa ta kafa kan cutar korona a Najeriya, Dr. Sani Aliyu.

Dr. Aliyu ya gargadi gwamnonin da su kaurace wa takara ko kuma yin gasa a tsakaninsu ta ganin samun adadin masu cutar korona a matsayin wata hanyar yin rige-rige.

Da yake ganawa da manema labarai a ranar Litinin cikin birnin Abuja, Dr. Aliyu ya bukaci gwamnonin da su kasance masu kwatanta gaskiya yayin bayyana adadin mutanen da cutar korona ta harba a jihohinsu.

Ya ce: "samun wani adadi na masu cutar korona ba abun yin gasa bane ko takara a tsakanin jihohi. Babu wani abun jin kunya idan wata jihar ta fito da adadi kadan ko mai yawa na masu cutar korona."

Dr. Sani Aliyu

Dr. Sani Aliyu
Source: Twitter

"Domin magance wannan annoba, muna bukatar jihohi su rika fadin gaskiya a yayin bayyana adadin mutanen da suka kamu da cutar komai yawansu komai kankanta."

"Muddin muka gaza sanin girman matsalar da take tunkaro mu, to kuwa ba ta yadda za a yi mu iya magance ta."

KARANTA KUMA: An samu bullar cutar korona karo na farko a jihar Nasarawa

“Don haka nake rokon gwamnatocin jihohi da su ci gaba da goyon baya tare da tallafawa cibiyoyin gudanar da ayyukan gaggawa da kuma ma’aikatun lafiya domin tabbatar da cewa duk wanda ke bukatar gwajin cutar korona a kowace jiha a kasar nan ya samu wannan dama."

Babban jami'in gwamnatin ya kuma ce har yanzu akwai jihohi da dama da ba su da wadatattun kayan aiki da karfin iko na dakile yaduwar cutar saboda haka a yanzu ne ya kamata a tashi farga tun kafin lamarin ya wuce gona da iri.

A yunkurin haka, ya ce kwamitinsu ya tabbatar da duk wata jiha a Najeriya ta wadatu da akalla gadaje 300 domin killace wadanda suka kamu da cutar cikin kowace jiha.

A halin yanzu dai hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, ta tabbatar da cewa mutane 1337 ne suka kamu da cutar korona a duk fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel