An kama matar da ta halaka uwar mijinta bayan ta caka ma ta wuka a jahar Neja

An kama matar da ta halaka uwar mijinta bayan ta caka ma ta wuka a jahar Neja

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Neja ta sanar da kama wata mata mai suna Fatima Sani mai shekaru 37 wanda take zargi da kashe uwar mijinta yar shekara 70, Aishatu Umar.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Yansandan sun kama Fatima ne a kauyen Gobirawa na karamar hukumar Mashegu, inji kwamishinan Yansanda, Adamu Usman ya bayyana.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Shehun Bama ya rasu yana da shekaru 63 a duniya

Kwamishinan ya bayyana haka ne a ranar Litinin a garin Minna, inda yace Fatima ta samu matsala ne da mijinta, Sani Umaru a ranar 23 ga watan Afrilu, wanda ta kai ga ya saketa.

Sai dai Fatima ta zargi uwar mijin da tunzura shi ya sake ta, da wannan ne ta shiga farautar ta, har ta tarar da ita a kauyen Tozon Daji, inda ta caka mata wuka, ta kashe ta har lahira.

An kama matar da ta halaka uwar mijinta bayan ta caka ma ta wuka a jahar Neja

An kama matar da ta halaka uwar mijinta bayan ta caka ma ta wuka a jahar Neja
Source: Depositphotos

Kwamishina Usman yace suna cigaba da gudanar da bincike game da lamarin, kuma da zarar sun kammala binciken za su gurfanar da ita gaban kotu domin ladabtarwa.

Ya kara da cewa sun samu labarin wasu yan bindiga a ranar 25 ga watan Afrilu da suka kai samame kauyen Tufa na karamar hukumar Gurara wanda suka yi musayar wuta da Yansanda.

Daga ciki an kama yan bindiga guda 3 da bindigar AK 47 guda 1 da kakin Sojoji, sai dai yace sun garzaya da su asibitin Umaru Musa Yar’aduwa dake Sabon Wuse sakamakon sun samu rauni.

Amma a asibitin likitoci suka tabbatar da mutuwarsu. Hakazalika Usman yace suna cigaba da farautar sauran yan bindigan, don haka ya nemi jama’a su taimaka musu da bayanan sirri.

A wani labari kuma, Wani magidanci da Womiloju tare da dansa, Taiwo sun fada hannun hukuma bayan an same su da laifin kashe wani matashin dan Fulani makiyayi.

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Ogun ne suka samu nasarar kama Uba da Dan, inda suke zarginsu da kashe wani bahillace, Abubakar Usman dan shekara 32.

Uba da Dan sun kashe Abubakar ne saboda ya kyale shanunsa sun shigar musu gona a kauyen Gbagba Elewure dake cikin karamar hukumar Odede na jahar Ogun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel