Mutuwar yawa: Fiye da mutane 700 sun mutu a kasar Iran bayan sun sha giya da sunan maganin Coronavirus

Mutuwar yawa: Fiye da mutane 700 sun mutu a kasar Iran bayan sun sha giya da sunan maganin Coronavirus

Fiye da mutane 700 ne suka gamu da ajalinsu bayan sun kwankwadi barasa a matsayin maganin annobar Coronavirus a kasar Iran, domin a tunaninsu giya tana maganin cutar.

Aljazeera ta ruwaito hukumar yaki da Coronavirus ta kasar Iran ce ta bayyana haka, inda tace mutane 728 ne suka mutu daga watan 20 ga watan Feburairu zuwa 17 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Shehun Bama ya rasu yana da shekaru 63 a duniya

Mutuwar yawa: Fiye da mutane 700 sun mutu a kasar Iran bayan sun sha giya da sunan maganin Coronavirus
Mutuwar yawa: Fiye da mutane 700 sun mutu a kasar Iran bayan sun sha giya da sunan maganin Coronavirus
Asali: Facebook

Gwamnatin Iran ta ce an samu karuwar mace mace daga shan barasa ninki 10 a shekarar daya data gabata, inda a shekarar 2019 aka samu mutane 66 da suka mutu sakamakon shan giya.

Kakaakin ma’aikatar kiwon lafiya na Iran, Kianoush Jahanpour ya ce mutane 5,011 ne suka kwankwadi sinadarin Methanol dake cikin giya, mutane 90 sun rasa idanunsu a dalilin haka.

Kasar Iran ita ce kan gaba a yankin gabas ta tsakiya wajen samun mace macen mutane a dalilin Coronavirus, inda mutane 5,086 suka mutu, yayin da ta kama wasu 91,000.

Ana sa sinadarin Methanol ne a cikin kayan shaye shaye, kuma yana janyo gabban mutum su yi sanyi tare da lalata kwakwalwa, alamunta sun hada da ciwon kirji da sauransu.

Sai dai gwamnatin kasar Iran ta nemi kamfanonin dake hada methanol zalla su kara masa kala ta yadda za’a zasu bambance shi daga ethanol, wanda ake wanke ciwo da shi.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kano ta bakin kwamishinan Muhammad Garba ta ce ta gano dalilan da suka kawo mace macen da aka dinga samu a jahar a makon da ta gabata.

A cewar gwamnatin jahar, mace macen na da alaka da cututtukan hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma cutar zazzabin cizon sauro da suka dade suna addabar jama’an jahar.

Garba yace sun gano haka ne bayan sun gudanar da cikakken bincike game da mace mace, don haka yace mace macen basu da alaka da Coronavirus, saboda haka kada jama’a su firgita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel