Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon kakakin majalisar jihar Jigawa rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon kakakin majalisar jihar Jigawa rasuwa

- Allah ya yi wa tsohon kakakin majalisar jihar Jigawa, Adamu Ahmed rasuwa

- Tsohon kakakin majalisar Jigawan ya rasu ne bayan jinyar da ya yi a asibiti

- Ahmed Adamu ya yi mulki ne zamanin tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido

Allah ya yi wa tsohon kakakin majalisar jihar Jigawa, Adamu Ahmed rasuwa.

Kamar yadda wani rahoto da jaridar Daily Post ta wallafa ya bayyana, tsohon kakakin majalisar jihar Jigawan ya rasu ne a asibiti sakamakon jinyar da ya sha.

Ahmed ya yi kakakin majalisar jihar Jigawa har sau biyu yayin mulkin tsohon gwamna Sule Lamido.

Ya kasance kakakin ne tun daga shekarar 2007 zuwa 2015.

Adamu Ahmed ya rasu ne yana da shekaru 66 a duniya.

Mansur Ahmad, mataimaki na musammman a fannin yada labarai ga tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya ce Ahmed ya rasu ne a jihar Kano a ranar Litinin bayan gajeriyar jinya.

Mamacin dan asalin garin Gurgun Daho ne da ke karamar hukumar Kafin Hausa na jihar Jigawa.

Ya yi kakakin majalisar jihar Jigawa din ne karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon kakakin majalisar jihar Jigawa rasuwa
Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon kakakin majalisar jihar Jigawa rasuwa
Asali: Twitter

KU KARANTA: APC da hukumar kwastam sun yi martani ga gwamnan PDP da zai mayar wa Buhari tallafi

Ahmed ya taba zama shugaban karamar hukumar Kafin Hausa kafin zuwansa majalisar jihar. Na hannun daman tsohon gwamna Sule Lamido ne.

Za a birnesa ne a garin Gurgun Daho da ke karamar hukumar Kafin Hausa ta jihar, kamar yadda addinin Islama ya tanadar.

Marigayin ya shiga jerin manyan mutanen da ke mutuwa a cikin jihar Kano.

Ya rasu ya bar matan aure biyu tare da 'ya'ya da jikoki.

A wani labari na daban, Wasu mazauna birnin Kano sun bayyana goyon bayansu a kan dokar hana walwala da shugaban Buhari ya saka wa jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, a ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada sanarwar rufe jihar saboda annobar Coronavirus.

Shugaban ya ce: "A dangane da jihar Kano, na bada umarnin rufe ta gaba daya na makonni biyu tun daga yanzu.

"Gwamnatin tarayya za ta tura duk wani abu da ake bukata don shawo kai da hana yaduwar annobar zuwa jihohin da ke makwabtaka da Kano."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel