COVID-19: Sabbin dokokin El-Rufa'i na kullen jihar Kaduna

COVID-19: Sabbin dokokin El-Rufa'i na kullen jihar Kaduna

A jiya ne gwamnatin jihar Kaduna ta sake sauya salon bude jihar na kwanaki biyu don siyayya kafin a ci gaba da zaman gida.

Daga yanzu za a dinga bude jihar ne a ranakun Laraba da Asabar don samun damar siyayyar abubuwan bukata.

A wata takarda da ta fito daga mai bada shawara ga gwamnan jihar na musamman a fannin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce wannan hukuncin an yanke shi ne bayan taron kwamitin yaki da cutar coronavirus na jihar, wanda mataimakiyar gwamna, Hadiza Balarabe ke shugabanta.

A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamna El-Rufai ya bayyana karin kwanaki 30 na rufe jihar bayan wata dayan da tayi a rufe.

Adekeye ya ce: "A ranar Laraba ta wannan makon, mazauna jihar masu sanye da takunkumin fuska ne kadai za su iya zuwa shaguna da kasuwannin abinci da magunguna".

Ya kara da cewa, "Dukkan kasuwanni za su kasance a rufe bayan ranakun Laraba. Sai kasuwannin wucin-gadi su ci gaba da ci har sai ranakun Asabar.

"Za a samarwa masu siyar da abinci da kuma magunguna wurare a makarantun gwamnati don samun damar siyarwa ga jama'a ba tare da cunkoso ba".

COVID-19: Sabbin dokokin El-Rufa'i na kullen jihar Kaduna
COVID-19: Sabbin dokokin El-Rufa'i na kullen jihar Kaduna
Asali: Facebook

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 5 a tawagar tsohon gwamnan Borno

Takardar ta bayyana cewa, kasuwannin wucin-gadin na jihar za su fara aiki ne daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma a ranakun Laraba da Asabar.

Hakazalika, za a kiyaye dokar nisantar juna a yayin da kasuwannin ke aiki.

Takardar ta kara da cewa, bayanai a kan inda za a kafa kasuwannin tare da dokokin da za a kiyaye za su fita babu dadewa.

Kafin nan, duk masu shagunan kayan abinci tare da magani za su iya budewa kowacce rana.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa kwamitin yaki da cutar coronavirus din ya amince da kyautatawa ga ma'aikatan lafiya na sahun gaba a yaki da annobar a asibitoci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel