Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 64 sun kamu da Coronavirus

Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 64 sun kamu da Coronavirus

Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da samun karin mutane 64 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Litinin, 27 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane sittin da hudu (64) sun kamu da #COVID19"

34-Lagos

15-FCT

11-Borno

2-Taraba

2-Gombe

A daidai karfe 11:20 na daren 27 ga Afrilu, an tabbatar da mutane 1,337 suka kamu da cutar COIVD-19 a Najeriya

Adadin wadanda aka sallama: 255

Adadin wadanda suka wafati: 40

A wani labarin daban, Jami'an tsaro tare da hadin gwuiwar jami'an gwamnatin Kaduna sun kama wasu manyan motocin dakon kayan abinci da aka boye mutane a cikinsu.

An kama motocin ne ranar Litinin a kauyen Sabon Gida da ke yankin karamar hukumar Ikara yayin da suke kokarin shiga jihar Kaduna.

Manyan motocin sun yi yunkurin shiga jihar Kaduna ne ta iyakarta da karamar hukumar Kiru ta jihar Kano.

Motocin sun yi basaja a zuwan sun dauko kayan abinci ne da zasu kai jihar Kaduna.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar Kaduna, ya ce jami'an tsaro sun kama motocin yayin da suke rangadin tabbatar da dokar hana zirga-zirga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel