Babu wata matsala da ka warware - PDP ta caccaki jawabin Buhari a kan annobar covid-19

Babu wata matsala da ka warware - PDP ta caccaki jawabin Buhari a kan annobar covid-19

Jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bai fadi wani abu da ya yiwa 'yan Najeriya dadi ba a cikin jawabin da ya gabatar kai tsaye da misalin karfe 8:00 na daren ranar Litinin.

Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi ne domin sanar da 'yan Najeriya halin da ake ciki dangane da yaki da annobar covid-19 a fadin kasa tare da sanar da daukan sabbin matakai a kan yanayin da ake ciki.

A cikin jawabin da sakataren yada labaranta, Kola Ologbondiyan, ya fitar a daren ranar Litinin, PDP ta ce shugaba Buhari bai zo da wani abu sabo a cikin jawabinsa ba.

PDP ta ce Buhari ya kara jaddada dokar rufe jihohi ne kawai, amma ba tare da yin bayani a kan yadda za a taimaki jama'a da masana'antun da tattalin arzikinsu ya karye saboda dokar ba.

A cewar PDP, fatan 'yan Najeriya shine samun mafita daga halin da kasa ta fada ciki, amma duk da haka ba a ji Buhari ya ambaci wata hanya da za a fitar da 'yan Najeriya daga wahala ba.

PDP ta ce shugaba Buhari ya ki daukan shawarar 'yan Najeriya ta yin amfani da masu ilimin kimiyyar lafiya, kimiyyar hada magunguna da sauran ma su ruwa da tsaki 'yan asalin kasa wajen tunkarar annobar.

Jam'iyyar ta ce, rashin daukan wannan shawara tun farko-farkon bullar annobar, shine silar fadawar Najeriya cikin halin da ake ciki a yanzu dangane da yaki da annobar covid-19.

"Kasar Senegal ta samu galaba a kan annobar covid-19 ta hanyar amfani da masananta na cikin gida. Yanzu ga shi suna kera kayan kiwon lafiya da ake bukata domin yaki da annobar.

"Bayan haka, sun fara samar da kayan gwajin cutar covid-19 a cikin kasarsu, gwamnatin kasar ta zuba kudi wajen sarrafa magungunan cikin gida da masana suka tabbatar suna da tasiri a kan kwayar cutar covid-19," a cewar jawabin PDP.

Kazalika, PDP ta ce ta fitar da rai daga tsammanin ganin wani abu na kirki ya fito daga kwamitin ko ta kwana da shugaba Buhari ya kafa domin yaki da annobar covid-19 a Najeriya.

A cewar PDP, shugaba Buhari ya bi siyasa ne kawai wajen nada mambobin kwamitin, wadanda akasarinsu basu da wata gogewa a bangaren shawo kan annoba balle dakileta.

"A saboda haka, mu na kira ga shugaban kasa da ya rushe kwamitin, sannan ya jingine banbacin siyasa, ya nada kwararru da suke da gogewa a bangare shawo kan annoba da dakile ta," a cewar PDP

PDP ta ce, shugaba Buhari ya dauki alkawarin samar da karin cibiyoyin gwaji, amma a gefe guda hukumar NCDC tana yekuwar neman kayan aiki a 'yan tsirarun cibiyoyin da ke aiki.

Jam'iyyar PDP ta ce ana yaudarar jama'a ne kawai.

A dangane da batun bayar da tallafi ga talakawa, PDP ta bukaci shugaba Buhari ya daina yaudarar 'yan Najeriya da alkawuran bogi, wadanda ba ya iya cikasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel