Gwamna Emmanuel ya koka game da ingancin abincin da gwamnatin tarayya take rabawa

Gwamna Emmanuel ya koka game da ingancin abincin da gwamnatin tarayya take rabawa

Gwamnan jahar Akwa Ibom, Emmanuel Udom ya bayyana tallafin abincin da gwamnatin tarayya ta aiko ma jama’an jaharsa basu da inganci ko kadan, ba zasu ciwu ba.

Daily Trust ta ruwaito Emmanuel ya bayyana haka ne a ranar Litinin a garin Uyo, inda yace buhunan shinkafa 1,800 da gwamnatin Buhari ta aiko musu a matsayin tallafi marasa kyau ne.

KU KARANTA: Uba da Da sun shiga hannu bayan sun kashe dan Fulani makiyayi a jahar Ogun

Sai dai gwamnan yace ba za su iya yin fatali da tallafin abincin ba sakamakon kyauta aka basu, kuma a al’adarsu basa mayar da hannu kyau baya, sai ya zamo butulci.

Idan za’a tuna gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana rashin ingancin abincin da gwamnatin tarayya ta aiko ma jama’an jaharsa, don haka yayi fatali da su, ya ki karba.

Gwamna Emmanuel ya koka game da ingancin abincin da gwamnatin tarayya take rabawa

Gwamna Emmanuel ya koka game da ingancin abincin da gwamnatin tarayya take rabawa
Source: Facebook

Shi ma dai Gwamna Emmanuel yace ba zai raba shinkafar nan ga jama’an jaharsa ba saboda kalar shinkafar ta canza, ya kara da cewa ya raba ma kowanne kauye a jahar tallafin abinci.

“Tallafin da muka samu daga gwamnatin tarayya kadai shi ne buhun shinkafa 1,800 wanda suka dade jibge a hannun hukumar kwastam, a yanzu haka shinkafar na can mu ma mun jibge ta, kyauta aka bamu.

“Mun aikata dakin gwaji domin a gwada ingancin ta, ba zamu raba ta ba saboda bata da kyau.” Inji shi.

A hannu guda, gwamnan ya bayyana cewa zuwa yanzu jahar Akwa Ibom ta samu mutane uku dake dauke da cutar Coronavirus, kuma a yanzu mutane 83 na jiran sakamakon gwaji.

Gwamnan yace asarar kudi ne kawai su yi ta yawon gwada mutanen da basu nuna wata alamar cutar ba, don haka yace babu yadda za’a yi su iya yi ma kowa gwaji a jahar.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kano ta bakin kwamishina Muhammad Garba ta ce ta gano dalilan da suka kawo mace macen da aka dinga samu a jahar a makon da ta gabata.

A cewar gwamnatin jahar, mace macen na da alaka da cututtukan hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma cutar zazzabib cizon sauro da suka dade suna addabar jama’an jahar.

Garba yace sun gano haka ne bayan sun gudanar da cikakken bincike game da mace mace, don haka yace mace macen basu da alaka da Coronavirus, saboda haka kada jama’a su firgita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel