Da duminsa: Sabbin Mutane 12 sun kamu da Coronavirus a Sokoto da Taraba

Da duminsa: Sabbin Mutane 12 sun kamu da Coronavirus a Sokoto da Taraba

Kwamitin kar ta kwana na yakar cutar Coronavirus a jihar Sokoto ta tabbatar da samun karin mutane takwas da suka kamu da cutar a jihar.

Shugaban kwmaitin wanda shine kwamishanan lafiyan jihar, Dakta Ali Inname, ya ce sabbin mutanen da suka kamu sun yi mu'amala da mutumin farko da ya kawo cutar jihar.

A cewarsa, mutane 28 su kayi mu'amala da mutumin amma mutane takwas cikinsu suka kwashi cutar daga jikinsa.

Ya ce dukkan maaikatan kiwon lafiyan da sukayi jinyarsa a asibitin koyarwan jami'ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto ne suka kamu.

Za ku tuna cewa shugaban kungiyar likitocin jihar, Dakta Muhammad Sani, ne mutumin farko da ya kamu da cutar a jihar.

Da duminsa: Sabbin Mutane 12 sun kamu da Coronavirus a Sokoto da Taraba

Da duminsa: Sabbin Mutane 12 sun kamu da Coronavirus a Sokoto da Taraba
Source: Twitter

A jihar Taraba kuwa, gwamnatin ta alanta kamuwar sabbin mutane shida da muguwar cutar Korona a jihar ranar Litinin.

Gwamnan jihar, Darius Ishaku, ya ce kada mutane su tayar da hankulansu kan hakan.

Yace mutanen shida da suka kamu na cikin mutane 130 da aka damke suna kokarin shiga jihar daga jihohin Legas, Borno, Bauchi, Kano, Jigawa da Ogun.

Ya ce za su cigaba da kulle dukkan iyakokin jihar kuma an umurci jamian tsaro kada su sake su bari wani ya shigo jihar.

Kawo yanzu, mutane 1,273 aka tabbatar suka kamu da cutar a Najeriya, kamar yadda cibiyar NCDC ta bayyana.

A bangare guda, Mun samu rahoton cewa, mahukuntan lafiya a jihar Kano sun sanar da karin mutane biyu da cutar korona ta hallaka a jihar.

A halin yanzu dai cutar korona ta yi sanadiyar ajalin mutane uku a jihar.

Ma'aikatar lafiyar jihar ce ta sanar da hakan da misalin karfe 12.15 na ranar Litinin, 27 ga Afrilun 2020 a kan shafinta na Twitter.

Taskar bayanai ta NCDC ta tabbatar da cewa, a halin yanzu dai mutane 1273 cutar corona ta harba a duk fadin Najeriya.

Har ila yau kuma jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan wadanda cutar ta kama inda adadinsu ya kai 731, sai kuma birnin tarayya inda cutar ta harbi mutum 141 yayin da jihar Kano ta biyo baya da mutum 77.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel