Yadda kasar Senegal ta yi zarra a nahiyar Afirka wajen yaki da cutar Coronavirus

Yadda kasar Senegal ta yi zarra a nahiyar Afirka wajen yaki da cutar Coronavirus

Gwamnatin kasar Senegal ta ciri tuta a tsakanin kasashen nahiyar Afirka a fafutukar da take yin a yaki da annobar Coronavirus ta hanyar amfani da sabbin kirkire kirkire da ta bullo da su.

Legit.ng ta ruwaito daga cikin kokarin da kasar Senegal ta yi akwai yi ma duk wani dan kasar ta gwajin cutar Coronavirus domin sanin matsayinsa, ko da ya nuna alamu ko bai nuna ba.

KU KARANTA: Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje 271 a jahar Kaduna

Haka zalika gwamnatin ta samar da kayan gwajin cutar masu saukin kudi da kuma aiki da karancin kuskure. Kayan gwajin da ta samar sun yi arhan da N360 zai sayi kayan gwaji daya.

Kasar bata tsaya nan, inda ta sake kirkiro wani na’urar agaza ma mara lafiyan wajen shakar numfashi mai sukin kudi mai suna 3D Printed Ventilator a kan kudi N2,163 duk guda daya.

Yadda kasar Senegal ta yi zarra a nahiyar Afirka wajen yaki da cutar Coronavirus
Yadda kasar Senegal ta yi zarra a nahiyar Afirka wajen yaki da cutar Coronavirus
Asali: UGC

Wannan hubbasa da gwamnatin kasar ta yi yasa ta kasance kan gaba wajen yawan mutanen da suka warke daga cutar Coronavirus a duk fadin nahiyar Afirka, kuma ita ce ta uku a duniya.

A hannu guda kuma, wani dan Najeriya dake zama a Birtaniya ya gargadi yan Najeriya su daina zagin shugaban kasa Muhammadu Buhari game da dokar ta hana shige da fice da ya sanya.

Mutumin mai suna Samuel N ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda yace ya kamu da cutar Coronavirus, kuma tsawon kwanaki 13 kenan bai iya cin abinci ba.

Don haka Samuel ya yi kira ga yan Najeriya da cewa Buhari na nufin su da alheri ne, domin kuwa a yanzu abin da ake nema shi ne a tsallake wannan annobar lafiya.

A wani labarin kuma, gwamnatin Kano ta bakin kwamishinan watsa labarunta, Muhammad Garba ta ce ta gano dalilan da suka kawo mace macen da aka dinga samu a jahar.

A cewar gwamnatin jahar, mace macen na da alaka da cututtukan hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma cutar zazzabib cizon sauro da suka dade suna addabar jama’an jahar.

Garba yace sun gano haka ne bayan sun gudanar da cikakken bincike game da mace mace, don haka yace mace macen basu da alaka da Coronavirus, saboda haka kada jama’a su firgita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng