Buhari zai gabatar da jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya da yammacin ranar Litinin

Buhari zai gabatar da jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya da yammacin ranar Litinin

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai gabatar da jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya da misalin karfe 8:00 na daren ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu.

Mataimaki na musamman ga shugaba Buhari, Buhari Sallau, ne ya sanar da hakan a shafinsa na dandalin sada zumunta (tuwita).

Za a iya kallon jawabin shugaba Buhari kai tsaye a gidan talabijin na kasa (NTA) ko saurarensa a gidajen radiyo na kasa (FRCN) da ke jihohin Najeriya.

Sanarwar ta bukaci sauran gidajen talabijin da radiyo na kasa su yada jawabin da shugaba Buhari zai gabatar.

Ana sa ran shugaba Buhari zai sanar da 'yan Najeriya halin da ake ciki a kasa dangane da yaki da annobar cutar covid-19.

Kazalika, ana sa ran zai yi bayani a kan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka danagane da yawaitar mace - macen jama'a a jihar Kano.

Jawabin na shugaba Buhari zai zo a daidai lokacin da dokar garkame wasu jihohi uku ta kare.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Jami'in gwamnati ya bayyana adadin mutanen da su ka mutu a cikin sati daya a Kano

A ranar Lahadi ne ministan lafiya, Osagie Enahire, ya sanar da cewa shugaba Buhari ne kadai ya ke da ikon yanke hukunci a kan dokar kulle jihohin.

Kungiyoyi da dama da suka hada da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) sun yi kira ga shugaba Buhari a kan kar ya kara wa'adin dokar rufe jihohin.

An samu barkewar wata kwarya - kwaryar zanga - zanga a jihar Legas bayan shugaba Buhari ya sanar da kara wa'adin dokar rufe jihohin a karo na farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel