Tashin hankali: Jami'in gwamnati ya bayyana adadin mutanen da su ka mutu a cikin sati daya a Kano

Tashin hankali: Jami'in gwamnati ya bayyana adadin mutanen da su ka mutu a cikin sati daya a Kano

Har yanzu rahotanni na cigaba da bayyana yadda ake cigaba da samun yawaitar mutuwar mutane a Kano duk da tabbacin da gwamnati ta bayar na cewa ta shawo kan lamarin.

A ranar Lahadi ne kwamishinan yada labarai a jihar Kano, Muhammad Garba, ya bukaci jama'a su kwantar da hankulansu tare da basu tabbacin cewa nan bada dadewa ba gwamnati za ta warware matsalar.

Mutane da dama sun mutu a cikin mako guda a jihar Kano.

A cewar Sabitu Shaibu, mataimakin shugaban kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 a jihar Kano, ya ce adadin mutanen da su ka mutu a Kano ya kai 640, kamar yadda jaridar 'TheCable' ta rawaito.

Wasu na zargin cewa annobar cutar covid-19 ce ke hallaka mutane a Kano.

Sai dai, a cewar Garba, mutane na mutuwa ne daga cututtuka irinsu hawan jini, zazzabi, ciwon sukari da sauransu.

Kazalika, mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tabbatar da cewa ba annobar covid-19 ce ke hallaka mutane a masarautarsa ba, kamar yadda wasu su ke zargi.

Tashin hankali: Jami'in gwamnati ya bayyana adadin mutanen da su ka mutu a cikin sati daya a Kano

Makabarta a Kano
Source: Twitter

A cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, Sarkin ya ce ma'aikatar lafiya ta jiha ta sanar da fadarsa cewa asarar dumbin rayukan da ake yi, ba sanadiyyar barkewar annobar cutar covid-19 bane.

Ya yi addu'ar Allah ya ji kan wadanda su ka mutu tare da yi wa marasa lafiya fatan samun sauki.

Da ya ke magana a kan annobar cutar covid-19, sarki Aminu ya yi kira ga mazauna Kano da su yi aiki da shawarwarin da hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) ta bayar a kan dakilye yaduwar covid-19.

DUBA WANNAN: An rasa wanda zai kawar da gawar da aka wayi gari da ganinta a gefen titi a Kano

Annobar yawaitar mace-mace ta lakume rayukan fitattun mutane a Kano da suka hada da manyan malaman jami'a da suka kai matakin Farfesa.

An sanar da mutuwar tsohon kwamishinan ilimi a jihar Kano, Aminu Yahaya, da Farfesa Balarabe Maikaba, a ranar Lahadi.

Mudi Mudi, babban jami'i a hukumar kula da makarantun sakandire ta Kano (KSSMB) ya mutu ranar Lahadi.

Asarar rayukan ba a iya kan fitattun mutane ta tsaya ba, dumbin talakawa sun mutu a Kano a 'yan kwanakin baya bayan nan.

Ministan lafiya, Osagie Enahire, ya ce gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zai binciko musabbabin yawaitar mutuwar mutane a Kano.

Kazalika, Femi Falana, babban lauya mai rajin kare hakkin bil'adama, ya bukaci gwamnatin tarayya ta sanar da jama'a sakamakon binciken kwamitinta da zarar kwamitin ya mika mata rahotonsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel