An rasa wanda zai dauki alhakin dauke gawar da aka wayi gari da ganinta a gefen titi a Kano

An rasa wanda zai dauki alhakin dauke gawar da aka wayi gari da ganinta a gefen titi a Kano

Mazauna yankin unguwar kofar Ruwa a jihar Kano sun wayi gari da samun gawar wani mutum a gefen titi, kamar yadda sashen Hausa na BBC ya rawaito.

Mazauna yankin, wanda ke makwabataka da barikin sojoji ta Bukavu, sun ce suna zargin gawar mutumin ta shafe kusan sa'a 24 a gefen titin.

BBC Hausa ta ce wani mazaunin unguwar ya sanar da ita cewa tun a ranar Juma'a su ka ga mutumin yana zaune a gefen titin da ya wuce har zuwa jihar Katsina daga cikin birnin Kano.

Majiyar ta bayyana cewa jama'a sun fara taruwa a kan gawar mutumin da misalin karfe 11 na safiyar ranar Asabar bayan sun tabbatar da cewa ya mutu.

Ya kara da cewa sun tuntubi jami'an gwamnati tare da sanar da su batun ganin gawar mutumin da basu san ko waye ba.

A cewar mutumin, "jami'an hukumar kwana - kwana na Bacirawa muka fara tuntuba amma sai suka ce yankin ba a karkashin kulawarsu yake ba."

An rasa wanda zai dauki alhakin dauke gawar da aka wayi gari da ganinta a gefen titi a Kano

Titi a Kano
Source: Facebook

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano ya shaidawa BBC cewa sun samu labarin ganin gawar amma ya ce kula da gawa hakkin jami'an lafiya ne, ba 'yan sanda ba.

Kazalika, mazauna unguwar sun bayyana cewa sun sanar da ofishin 'yan sanda na Dala, amma sai suka shaida musu cewa su tuntubi ma'ikatar lafiya.

"Duk lambobin hukumar NCDC da muka kira babu wacce ta shiga," a cewar Benjamin, wani mazaunin yankin a hirarsa da BBC.

DUBA WANNAN: Mahaifiyar Ado Gwanja da sauran fitattun mutane 15 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 a Kano

Benjamin ya ce sun sanar da mai unguwar Dala, sannan sun je asibitin Murtla amma babu wanda ya yi wani abu a kan gawar.

A cewarsa, gawar ta kai har karfe 12:30 na ranar Asabar amma babu wasu jami'ai da suka zo wurin.

Legit.ng ta wallafa rahotanni a kan yadda jama'ar Kano ke zaune cikin zulumi sakamakon yawaitar mutuwar mutane, yawancinsu dattijai.

Jama'a na cigaba da kiraye - kiraye a kan gwamnati ta gudanar da bincike a kan yawaitar mace - macen da ake samu a jihar Kano.

Babu wata hujja da ta nuna cewa mutanen da ke mutuwa sun kamu da kwayar cutar covid-19 duk da annobar ta bulla jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel