Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 5 a tawagar tsohon gwamnan Borno

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 5 a tawagar tsohon gwamnan Borno

- A ranar Alhamis ne mayakan ta'addanci na Boko Haram suka tare tawagar tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff a kan hanyar Maiduguri

- Bayan musayar ruwan wuta da aka yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan ta'addan, mutum 5 sun rasa ransu daga cikin tawagar Sanatan

- Kamar yadda majiya daga jami'an tsaro ta bayyana, an kai wa sanatan harin ne garin Auno yayin da yake kan hanyar zuwa sadakar ukun mahaifinsa

Mayakan ta'addanci na Boko Haram sun kashe mutum 5 a tawagar tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Wata majiya daga jami'an tsaro ta ce 'yan ta'addan sun hari tawagar Sheriff ne a garin Auno, kilomita kadan zuwa Maiduguri.

Majiyar ta ce Sheriff na kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri daga Abuja a yammacin ranar Alhamis.

Yana kokarin zuwa sadakar uku ta mahaifinsa, Galadima Sheriff, wanda ya rasu a makon da ya gabata.

Ya ce Sheriff na tafe ne da tawagar kasaitattun motoci guda tara a jere.

Mayakan ta'addancin sun tare tawagar Sheriff ne a garin Auno inda suka fara musayar wuta da jami'an tsaron da yake tare da su.

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 5 a tawagar tsohon gwamnan Borno

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 5 a tawagar tsohon gwamnan Borno
Source: Twitter

KU KARANTA: A kan gado: Matashi ya soka wa mahaifiyarsa wuka tare da banka mata wuta

Sun fara musayar wutar ne wurin karfe 6:30 na yammaci amma sai 'yan sanda biyu, farar hula biyu da kuma soja guda daya suka rasa rayukansu.

Kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa, majiyar ta ce an tarwatsa daya daga cikin motocin alfarmar da suke tare da ita kafin jami'an tsaro su iso.

Majiyar ta ce jami'an tsaron da suka isa ne suka fatattaki mayakan ta'addancin.

Wannan ne karo na farko da 'yan ta'addan suka samu nasarar tare tsohon gwamnan duk da cewa sun saba yi masa barazanar hakan.

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau na nuna alamun mika wuya ga dakarun.

Kamar yadda rundunar ta bayyana, za ta karba shugaban 'yan ta'addan matukar ya mika wuya tare da ajiye makamansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel