APC da hukumar kwastam sun yi martani ga gwamnan PDP da zai mayar wa Buhari tallafi

APC da hukumar kwastam sun yi martani ga gwamnan PDP da zai mayar wa Buhari tallafi

Jam'iyyar APC da hukumar kwastam ta kasa ta yankin Oyo/Osun a ranar Asabar sun kwatanta ikirarin gwamnatin jihar Oyo da rashin gaskiya.

Idan za mu tuna, gwamnatin tarayya ta bai wa gwamnatin jihar Oyo buhu 1,800 na shinkafa don tallafi ga mabukata da talakawan jihar.

Amma kuma a ranar Juma'a da ta gabata sai gwamnatin jihar ta fito ta bayyana cewa za ta mayar wa gwamnatin tarayya shinkafar don duk ta lalace da kwari.

APC da hukumar kwastam din ta kasa, sun ce shinkafar lafiyayya ce kuma babu wani abu da ya sameta kamar yadda gwamnan jihar, Seyi Makinde ya yi ikirari.

Jam'iyyar APC ta ce wannan wani yunkuri ne na siyasantar da tallafin da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar.

A wata takardar da jam'iyyar ta fitar a ranar Asabar ta hannun sakataren yada labaranta, Abdulazeez Olatunde, ya ce "Mun gano cewa wannan wani yunkuri ne na saka siyasa cikin tallafin da aka bada don rage radadi ga talakawan jihar Oyo."

APC da hukumar kwastam sun yi martani ga gwamnan PDP da zai mayar wa Buhari tallafi

APC da hukumar kwastam sun yi martani ga gwamnan PDP da zai mayar wa Buhari tallafi
Source: Facebook

KU KARANTA: Dakarun sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 89 a Zamfara, sun halaka wasu a Katsina

Hakazalika, jami'in hulda da jama'a na hukumar kwastam din yankin, Abdullahi Musa, ya ce ba gaskiya bane zancen.

Musa ya ce, "Mai girma mataimakin gwamnan a fannin harkar gona, Dr Debo Akande tare da mataimaki na musamman ga gwamnan a kan harkar tsaro, Fatai Owoseni sun fara zuwa duba shinkafar a ofishinmu kafin a kai musu ita.

"Mun matukar girgiza da muka ji sun ce ba za ta ciwu ba don duk ta lalace. Shinkafar na lafiya kalau. Ta ya ya za mu saki lalatacciyar shinkafa ga jama'a. Abun da bada haushi.

"Hukumar kwastam ta jihar Oyo/Osun tana da wurin adana kaya biyu ne. Da kansu suka zaba shinkafar da suke so don a kai musu. Sun zaba ne kafin sauran jihohin."

Kakakin hukumar ya tabbatar da cewa ana ta kokarin shawo kan matasalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel