A kan gado: Matashi ya soka wa mahaifiyarsa wuka tare da banka mata wuta

A kan gado: Matashi ya soka wa mahaifiyarsa wuka tare da banka mata wuta

- Wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Johnbosco Ejiogu ya yi yunkurin halaka mahaifiyarsa a karamar hukumar Mbaitoli

- Matashin ya rufe kanshi da mahaifiyarsa a cikin gida inda ya soka mata wuka tare da bankawa gidan wuta

- An gano cewa, mahaifiyarsa ta shawarcesa ne da ya daina siyar da kadarorin gadon shi, lamarin da ya tunzura shi

Wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Johnbosco Ejiogu da ke Umudagu Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo ya shiga hannun 'yan sanda.

Ana zargin mutumin ne da yunkurin kashe mahaifiyarsa mai suna Pauline Ejiogu.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a bayan mahaifiyar ta shawarci dan ta a kan kada ya siyar da gadon shi.

Fusatar da Johnbosco ya yi ce ta sa ya kullesu biyu a cikin gida tare da soka mata wuka. Bayan nan ne ya bankawa gidan wuta.

Amma kuma, taimakon gaggawa da 'yan kauyen suka kai ne tare da 'yan achaba yasa suka kashe wutar.

Tuni suka kwashesu zuwa asibiti don gaggauta ceto rayuwarsu, jaridar Leadership ta ruwaito.

A kan gado: Matashi ya soka wa mahaifiyarsa wuka tare da banka mata wuta

A kan gado: Matashi ya soka wa mahaifiyarsa wuka tare da banka mata wuta
Source: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Covid-19 ta kashe kwararren ma'aikacin banki a Kano

Wani makwabcinsu mai suna Ikenna ya sanar da jaridar Leadership cewa laifin Ejiogu daya shine nasihar da ta yi wa danta a kan ya sauya rayuwarsa tare da daina siyar da kadarorin gadonsa.

Kamar yadda yace, Johnbosco ya saba bai wa mahaifiyarsa wahala saboda rashin jinsa.

Tuni dai rundunar 'yan sandan jihar suka tabbatar da samun rahoton.

Kakakin rundunar, Orlando Ikeokwu ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

A wani labari na daban, wata mata da ake zargin ta tsere ne daga cibiyar killacewa ta Abuja an damke ta a jihar Nasarawa.

Matar 'yar asalin Ibadan ce kuma ana zargin ta gudu daga cibiyar killacewa ne da ke Abuja inda ta tunkari jihar Nasarawa.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, wata majiya ta ce, "Na samu kira daga jami'an tsaro daga Abuja a kan cewa suna bibiyar wata mata da ta tsere daga cibiyar killacewa ta Abuja da ke Akwanga.

"Ina samun kiran na dauka mataki ta hanyar kiran mutanena da ke kauyen Kurmin Tagwaye a Akwanga. Sun gano matar har gidanta,"

An je har gida an kama ta a kusa da cocin ERCC da ke Kurmin Tagwaye a kan titin Wamba da ke Akwanga. Daga nan ne aka mika ta cibiyar killacewa da ke babban asibitin garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel