Covid-19: An damke matar ta kubce daga cibiyar killacewa a Abuja a jihar Nasarawa

Covid-19: An damke matar ta kubce daga cibiyar killacewa a Abuja a jihar Nasarawa

Wata mata da ake zargin ta tsere ne daga cibiyar killacewa ta Abuja an damke ta a jihar Nasarawa.

Matar 'yar asalin Ibadan ce kuma ana zargin ta gudu daga cibiyar killacewa ne da ke Abuja inda ta tunkari jihar Nasarawa.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, wata majiya ta ce, "Na samu kira daga jami'an tsaro daga Abuja a kan cewa suna bibiyar wata mata da ta tsere daga cibiyar killacewa ta Abuja da ke Akwanga.

"Ina samun kiran na dauka mataki ta hanyar kiran mutanena da ke kauyen Kurmin Tagwaye a Akwanga. Sun gano matar har gidanta,"

An je har gida an kama ta a kusa da cocin ERCC da ke Kurmin Tagwaye a kan titin Wamba da ke Akwanga.

Daga nan ne aka mika ta cibiyar killacewa da ke babban asibitin garin.

Hakazalika, wasu mutum biyu da ake zargin suna dauke da cutar coronavirus an killacesu a babban asibitin Akwanga da ke jihar Nasarawa.

Daya daga cikin marasa lafiyar dan asalin garin Rinze ne na karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.

Dayan kuwa har yanzu ba a tabbatar da garinsu ba.

Wata majiya ta ce an fara kai mutum na farkon ne a ranar Alhamis yayin da aka kai na biyun a ranar Asabar da safe.

Har yanzu dai jihar Nasarawa ba ta tabbatar da kamuwa koda mutum daya na jihar da muguwar cutar ba.

Kwamishinan lafiya na jihar, Pharm Mohammed Abmed Yahaya ya ce, "Mun killace wasu mutane amma har yanzu ba a tabbatar da cewa suna dauke da cutar bane. Muna jiran sakamako."

Covid-19: An damke matar ta kubce daga cibiyar killacewa a Abuja a jihar Nasarawa
Covid-19: An damke matar ta kubce daga cibiyar killacewa a Abuja a jihar Nasarawa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Kano: Yadda 'yan anguwa suka kwace kayan tallafi daga 'yan kwamitin rabo (Bidiyo)

A wani labari na daban, A matsayin hanyar tabbatar da dokar nisantar juna ta yi aiki a kasuwannin Abuja tare da hana yaduwar annobar a babban birnin tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya bada umarnin cewa dole a yi amfani da takunkumin fuska a kasuwanni.

Ministan ya kara da umartar hukumar kula da kasuwannin Abuja cewa, su kirkiri wurin siyayya 40 a fadin birnin don rage cunkoson da kasuwannin ke fuskanta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Manajan daraktan hukumar, Abubakar Usman Faruk, wanda ya zanta da manema labarai a jiya, ya ce ministan ya amince da kara sa'o'in kasuwa daga karfe 8 na safe zuwa 3 na yamma a ranakun Laraba da Asabar.

"Wannan umarnin zai fara aiki ne a ranar 25 ga watan Afirilun 2020. Ministan ya jaddada cewa duk masu shiga kasuwar sai sun yi amfani da takunkumin fuska tare da bin dokokin nisantar juna.

"A yayin da yake shawartar mazauna birnin tarayya da su goyi bayan dokar hana zirga-zirgar, ya umarci jami'an tsaro da su damke duk wanda ya take dokar gwamnatin a kasuwannin," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel