Mahaifiyar Ado Gwanja da sauran fitattun mutane 15 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 a Kano

Mahaifiyar Ado Gwanja da sauran fitattun mutane 15 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 a Kano

Jama'ar Kano na zaune cikin fargaba saboda yawaitar mace - macen mutane, yawancinsu tsoffi, da ake samau a cikin birnin jihar.

Tun a makon jiya gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya saka dokar kulle jihar Kano; ba shiga, ba fita, sannan jama'a ma ba za su fito daga gidajensu ba.

Gwamnatin jihar ta dauki wannan tsatsauran mataki ne biyo bayan bullar annobar covid-19 a jihar.

Duk da gwamnatin Kano ta musanta labarin yawaitar mutuwar mutane a cikin birnin jihar, rahotanni sun bayyana cewa adadin mutanen da ke mutuwa ya na cigaba da aruwa.

An samu mutuwar mutane da dama a cikin birnin Kano da kewaye daga yammacin ranar Juma'a zuwa ranar Asabar da rana.

Fitattu daga cikin wadanda su ka mutu akwai: tsohon kwamishina a jihar Kano; Farfesa Ibrahim Ayagi, editan jaridar Triump; Musa Ahmad Tijjani, tsohon shugaban hukumar ma'aikatan jihar Kano; Adamu Dal

Sauran sune: Nasiru Maikano Bichi, Musa Umar Gwarzo, Ustaz Dahiru Rabi'u, tsohon alkali; Khadi Salisu Lado, Nene Umma, Garba Sarki Fagge, Salisu Lado, Shamsiyya Mustapha, Nene Umma, Garba Sarki Fagge, Rabiu Dambatta, Kabiru Ibrahim Bayero da mahaifiyar fitaccen mawaki, Ado Gwanja.

Gwanja da kansa ya sanar da mutuwar mahaifiyarsa a shafinsa na dandalin sada zumunta, wato 'facebook', inda masoyansa su ka taya shi jaje tare da aika sakon ta'aziyyarsu.

Legit.nt ta wallafa rahoton labarin mutuwar Fitaccen masanin ilimin tattalin arziki, Farfesa Ibrahim Ayagi, wanda ya mutu ranar Asabar a jihar Kano.

An haifi marigayi Ayagi a shekarar 1940 a jihar Kano, ya mutu yana da shekara 80 a duniya bayan ya sha fama da rashin lafiya.

DUBA WANNAN: Covid-19: Kura-kurai 7 da 'yan Najeriya ke tafkawa wajen amfani da takunkumi

An yi jana'izarsa bayan sallar La'asar a gidansa da ke kallon makarantar sakandiren Gwale a cikin garin Kano.

Marigayi Ayagi, wanda ake girmamawa saboda iliminsa a bangaren tattalin arziki, ya taba rike babban darektan bankin 'Continental Merchant Bank'.

Farfesa Ayagi ya taba rike kujerar kwamishinan cigaban tattalin arzikin jihar Kano daga shekarar 1975 zuwa 1978.

Kazalika, ya rike mukamin babban darektan gidauniyar jihar Kano (Kano Foundation) daga shekarar 1987 zuwa 1990.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel