Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 87sun kamu da Coronavirus, 18 a Borno
Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da samun karin mutane 87 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Asabar, 25 ga Afrilu, 2020.
Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane tamanin da bakwai(87) sun kamu da #COVID19"
33 a Lagos
18 a Borno
12 a Osun
9 a Katsina
4 a Kano
4 a Ekiti
3 a Edo
3 a Bauchi
1 a Imo
A daidai karfe 11:30 na 25 ga Afrilu, an tabbatar kamuwar mutane 1182 da cutar COVID-19 a Najeriya
An sallmi: 222
Mutuwa: 35
KU KARNATA: COVID-19: Budurwa roki NCDC ta kama mahaifiyarta saboda karya dokar zaman gida a Nasarawa
Kawo yanzu, ga jerin jihohin da cutar ta bulla da adadinsu:
Lagos-689
FCT-138
Kano-77
Ogun-35
Osun-32
Gombe-30
Katsina-30
Borno-30
Edo-22
Oyo-18
Kwara-11
Akwa Ibom-11
Bauchi-11
Kaduna-10
Ekiti-8
Ondo-4
Delta-6
Rivers-3
Jigawa-2
Enugu-2
Niger-2
Abia-2
Zamfara-2
Sokoto-2
Benue-1
Anambra-1
Adamawa-1
Plateau-1
Imo-1
A bangare guda, Allah ya yi wa tsohon babban alkalin kotun daukaka karar shari'ar Musulunci ta jihar Kano, Dahiru Rabiu rasuwa.
Ya rasu ne a yau Asabar a gidansa da ke kwatas din Galadanci a cikin garin Kano.
Daya daga cikin iyalan mamacin ne ya sanar wa jaridar Leadership. Ya ce za a kai mamacin makwancinsa a yau bayan an kammala tanadin addinin Musulunci a kan gawar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng