Kano: Yadda 'yan anguwa suka kwace kayan tallafi daga 'yan kwamitin rabo (Bidiyo)

Kano: Yadda 'yan anguwa suka kwace kayan tallafi daga 'yan kwamitin rabo (Bidiyo)

Mazauna wata anguwa a jihar Kano sun tare masu rabon kayan tallafi na jihar inda suka dinga kwatar kwalaye da buhunan kayan abinci.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, an ga jama'a na tururuwar dibar kwalaye tare da sauke buhu a gefe.

An ga motar na gudu amma 'yan anguwar na biye da ita inda suke dibar kayan daga cikin motar.

Daga bisani kuma an ga jama'ar na tsayar da ababen hawa inda suke shigewa tare da kayan da suka diba daga motar.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Covid-19 ta kashe kwararren ma'aikacin banki a Kano

A wani labari na daban, Wani shugaban babban banki da ke jihar Kano, Abdullahi Lawal ya mutu bayan an zargi yana dauke da cutar Covid-19.

Majiya daga iyalansa ta ce marigayin kuma kwararren ma'aikacin bankin, ya fara ciwo ne a ranar Juma'a, jaridar The Nation ta wallafa.

An fara kwantar da shi ne a ranar a wani asibitin kudi inda daga nan aka tura shi asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Majiyar ta ce, Lawal na cikin shekarunsa na 50 ne da doriya kuma an hanzarta kai shi asibitin mai zaman kansa ne bayan zazzabi mai zabi, tari da kuma sarkewar numfashi sun tsananta a gareshi.

Kamar yadda majiyar ta ce, bayan isarsu asibiti, an saka mishi naurar taimakon numfashi a asibitin mai zaman kansa amma sai suka cire bayan sun ga babu alamun sauki da yake zuwa.

Wata mata mai suna Hajiya Salma Ahmed wacce ta ce ita ce sirikar marigayin, ta saki wani sakon sautin murya inda take jajanta rashin kula da hukumar kula da cututtuka masu yaduwa suka nuna musu.

Hajiya Salma ta ce "Iyalansa sun dinga kiran NCDC ta kano amma layin baya tafiya. Daga karshe sai suka kira na Abuja sannan suka samu tabbacin cewa jami'an hukumar da ke Kano za su har gida don diban samfur.

"Amma babu wanda ya kawo ziyara har sirikina ya mutu a cikin tsananin ciwon da bai tashi ba."

Hajiya Salma ta nuna damuwarta don a tunaninta diyarta da sauran iyalan marigayin sun kwashi kwayar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel