COVID-19: A karo na farko, an samu bullar Korona a Zamfara

COVID-19: A karo na farko, an samu bullar Korona a Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya tabbatar da cewa mutane biyu sun kamu da kwayar cutar COVID-19 a jihar kamar yadda premium Times ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ke sanar da cewa ta siya naurar ventilator 12 da kayan gwajin cutar 20,000 da za a ajiye a sansanin killace masu cutar a cewar kakakin gwamnan, Zailani Bappa.

A sakon da gwamnan ya fitar cikin dare a faifan bidiyo, ya ce gwajin da hukumar NCDC ta yi wa wasu mutane a jihar ya nuna mutum biyu sun kamu da cutar.

Gwamnan ya ce sakamakon gwajin ya nuna cewa gwamnatinsa ba azarbabi ta yi ba wurin daukan dokoki na kare yaduwar cutar a jihar tun kafin a gano bullar ta a jihar.

COVID-19: A koro na farko, an samu bullar Korona a Zamfara
COVID-19: A koro na farko, an samu bullar Korona a Zamfara
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama mutumin da ya haike wa matarsa har ta mutu a Jigawa

Matawalle ya sanar da cewa, "Anjima zan sanar da karin matakan da za a dauka domin kare mutanen jihar mu daga wannan mummunan cutar mai kisa."

Ya yi kira da mutanen jihar su kasance masu kulawa da bin dokokin nesantar juna da amfani da takunkumin fuska da man kashe kwayoyin cuta wato sanitizer.

Da ya ke duba kayayakin da aka siyo a sansanin killace mutane da ke Asibitin Kwararru na Yariman Bakura a Gusau, Matawalle ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da yin duk mai yiwuwa don kare mutanen jihar daga annobar.

Sauran kayayyakin da aka siyo sun hada da hand sanitizer da takunkumin rufe fuska da za a raba wa mutane a fadin jihar.

Matawalle ya shawarci mutane su bi dokokin da aka saka yayin azumin Ramadana domin hakan ne kawai hanyar da mutane za su dakile yaduwar cutar.

Ya ce rufe iyakokin jihar da hana tafsiri da sauran matakan da aka dauka duk an yi ne da niyya mai kyau ba don musgunawa mutane ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel