Saudiyya ta haramta hukuncin bulala ga masu laifi

Saudiyya ta haramta hukuncin bulala ga masu laifi

– Kasar Saudiyya ta haramta wa alkalan yanke hukuncin bulala ga masu laifi a kasar

– Kotun koli kasar ne ta bayar da wannan sanarwar cikin sauye sauye da kasar ke yi don shiga sahun sauran kasashe masu raji kare hakkin dan adam

– Hakan na nufin yanzu alkalai sai da su yanke wa masu laifi hukuncin gidan yari, tara ko ayyukan al'umma

Saudiyya ta soke yin bulala a matsayin hukunci ga masu laifi a kasar kamar yadda kotun koli na kasar sanar cikin sauye sauyen da sarkin kasar da dan sa yarima mai jiran gado su ke yi.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun dade suna sukar hukuncin bulala da kotuna a kasar ke yanke wa masu laifi inda wasu lokutan ake yi wa mutane bulala fiye da 1OO.

Saudiyya ta haramta hukuncin bulala ga masu laifi
Saudiyya ta haramta hukuncin bulala ga masu laifi
Asali: Twitter

Kotun kolin na Saudiyya ta ce an yi wannan canjin ne domin daidai ta dokokin kasar da na kasashen duniya masu rajjin kare hakkin yan adam da hana hukuncin kisa.

DUBA WANNAN: An kama mutumin da ya haike wa matarsa har ta mutu a Jigawa

A baya, alkalan kotu suna iya yanke wa wadanda aka samu da laifuka kamar zina, tayar da hankulan mutane ko kisa hukuncin bulala.

Daga yanzu, alkalan ba su da wata zabi da ya wuce cin tara, hukuncin dauri da sauran hukunci da suka hada da yi wa al'umma hidima da dai sauransu kamar yadda AFP ta ruwaito a ranar Asabar.

Hukuncin bulala mafi tsanani na baya bayan nan shine wanda ake yanke wa wani marubuci a Saudiyya, Raif Badawi inda aka yanke masa hukuncin bulala 1,OOO da hukuncin gidan yari na shekaru 1O a 2O14 saboda yi wa musulunci izgili.

An karrama shi da lambar yabo da hakin dan adam na Sakharov a shekarar 2O15.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel