Da duminsa: Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Edo ya yi murabus

Da duminsa: Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Edo ya yi murabus

Taiwo Akerele, shugaban ma'aikatan Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya yi murabus daga mukaminsa.

A wasikar da ta bayyana mai kwanan wata 25 ga watan Afirilu, ya yi ta ne ga gwamnan inda ya ce wannan hukuncinsa ya yanke shi ne saboda "yanayin shugabancin da ake yi."

Tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Oyo din ya ce zai ci gaba da goyon bayan duk wani kokari na gwamnan na tabbatar da ci gaban jihar.

Amma kuma zai so a bashi dama ce irin ta "mai zaman kansa."

"Hukuncina na barin gwamnatin ya biyo bayan yanayin tsari da mulkin da ake yi ne," wasikar ta ce.

Wasikar ta ce, "Ina tare da mai girma Godwin Obaseki a duk wani kokarinsa na kawo gyara a jihar Edo. Yanayin tsarinsa da hangensa duk irin nawa ne.

"Abinda kawai zan iya cewa shine a bani damar yi wa jihar aiki amma a matsayin mai zaman kansa ba ma'aikacin gwamnatin ba.

"Ina godiya ga mai girma gwamna da ya bani damar aiki tare da shi. Ina mika godiya ga mai martaba Oba na Benin, Oba Ewuare II a kan shugabancinsa da kuma goyon baya a lokacin da nayi aiki."

Da duminsa: Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Edo ya yi murabus

Da duminsa: Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Edo ya yi murabus
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Covid-19: Gwamnan PDP zai mayar wa Buhari mota uku ta shinkafa da ya ba jiharsa tallafi

A yayin tsokaci a kan wannan ci gabna, Crusoe Osagie, mataimaki na musamman ga gwamna afannin yada labarai, ya ce har yanzu dai Obaseki bai samu wasikar murabus din ba.

Osagie ya ce gwamnan zai amince da wasikar matukar ta isa wurinsa, jaridar The Cable ta ruwaito.

"A sa'o'i kadan da suka gabata ne na ga cewa shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Oyo ya yi murabus a kafafen sada zumuntar zamani," takardar tace.

"A yayin da gwamnan bai samu wasikar ba ko wani nau'i na sadarwa da ke nuna hakan, wannan hukuncin na Akerele ne.

"Amma kuma, duk lokacin da ya samu wasikar murabus din, zai amince da ita tare da yi wa Akerele fatan alheri a rayuwarsa," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel