Covid-19: Minstan FCT ya saka sabuwar doka a kasuwanni

Covid-19: Minstan FCT ya saka sabuwar doka a kasuwanni

- A kokarin tabbatar da hana yaduwar muguwar annobar Covid-19 a birnin tarayya da kasa baki daya, ministan FCT ya saka wata sabuwar doka

- Kamar yadda ya bayyana ga hukumar kula da kasuwannin Abuja, dole ne masu siye da siyarwa a kasuwannin su saka takunkumin fuska kafin shiga kasuwar

- Ministan ya jaddada cewa, duk wanda aka kama da laifin take dokar, za a damke shi tare da sa shi ya fuskanci hukuncin da ya dace

A matsayin hanyar tabbatar da dokar nisantar juna ta yi aiki a kasuwannin Abuja tare da hana yaduwar annobar a babban birnin tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya bada umarnin cewa dole a yi amfani da takunkumin fuska a kasuwanni.

Ministan ya kara da umartar hukumar kula da kasuwannin Abuja cewa, su kirkiri wurin siyayya 40 a fadin birnin don rage cunkoson da kasuwannin ke fuskanta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Manajan daraktan hukumar, Abubakar Usman Faruk, wanda ya zanta da manema labarai a jiya, ya ce ministan ya amince da kara sa'o'in kasuwa daga karfe 8 na safe zuwa 3 na yamma a ranakun Laraba da Asabar.

Covid-19: Minstan FCT ya saka sabuwar doka a kasuwanni

Covid-19: Minstan FCT ya saka sabuwar doka a kasuwanni
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Kano: Ana ci gaba rasa rayuka duk da musantawar gwamnati

"Wannan umarnin zai fara aiki ne a ranar 25 ga watan Afirilun 2020. Ministan ya jaddada cewa duk masu shiga kasuwar sai sun yi amfani da takunkumin fuska tare da bin dokokin nisantar juna.

"A yayin da yake shawartar mazauna birnin tarayya da su goyi bayan dokar hana zirga-zirgar, ya umarci jami'an tsaro da su damke duk wanda ya take dokar gwamnatin a kasuwannin," yace.

A wani labari na daban, a yayin da gwamnatin jihar Kano ke ci gaba da musanta mutuwar jama'ar jihar, mazauna birnin na zaune a cikin tsoro ne don kuwa ana ci gaba da birne gawawwaki ba kamar yadda aka saba ba.

Bayan jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an birne mutum 150 a cikin kwanaki uku kacal, gwamnatin jihar ta fito ta musanta.

Amma kuma mazauna garin suna ci gaba da fuskantar irin wannan mutuwar da birne gawawwaki ba kamar yadda aka saba ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel