Kano: Ana ci gaba rasa rayuka duk da musantawar gwamnati

Kano: Ana ci gaba rasa rayuka duk da musantawar gwamnati

A yayin da gwamnatin jihar Kano ke ci gaba da musanta mutuwar jama'ar jihar, mazauna birnin na zaune a cikin tsoro ne don kuwa ana ci gaba da birne gawawwaki ba kamar yadda aka saba ba.

Bayan jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an birne mutum 150 a cikin kwanaki uku kacal, gwamnatin jihar ta fito ta musanta.

Amma kuma mazauna garin suna ci gaba da fuskantar irin wannan mutuwar da birne gawawwaki ba kamar yadda aka saba ba.

Wasu mazauna garin da suka zanta da jaridar Daily Trust sun ce an samu sauki a kan hakan amma fa ana ci gaba da sallar Janaza ta mutane masu tarin yawa wadanda cutar zazzabin cizon sauro da taifot ya kashe.

A yankin Zangon Barebari kadai, an gano cewa a kalla mutum 15 ne suka rasu tsakanin ranar Laraba da Juma'a.

Hakazalika, wani mai tsaron makabartar Dandolo ya sanar da jaridar Daily Trust cewa yana da tabbacin cewa yawan mace-macen da ake yi karuwa yake ba raguwa ba.

"Tsakanin Laraba da Alhamis, mun birne a kalla gawawwaki 67," yace.

Kamar yadda wasu iyalai suka bayyana, sakamakon barkewar annobar Coronavirus a jihar, 'yan uwansu basu iya zuwa asibiti don a duba lafiyarsa wanda hakan ke zama sanadin mutuwarsu..

Daily Trust ta gano cewa, manyan asibitocin jihar da suka hada da asibitin Malam Aminu Kano, sun dakatar da ayyukansu saboda samun damar karkata kan annobar.

Kano: Ana ci gaba rasa rayuka duk da musantawar gwamnati
Kano: Ana ci gaba rasa rayuka duk da musantawar gwamnati
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda marigayi Abba Kyari ya kusan zama mataimakin Obasanjo a 1999 - Mamman Daura

Mustapha Muhammad Zakari, mazaunin kwatas din Gwammaja ne da ke karamar hukumar Dala wanda ya rasa mahaifiyarsa a kwanakin nan.

Ya ce mahaifiyarsa ta kasance da ciwon suga amma ta rasu ne bayan asibitin kashi da ke Dala sun ki karbarta.

"Na kusan shekara daya, mahaifiyata na fama da ciwon suga kuma tana zuwa asibitin kudi ne.

"Sakamakon barkewar annobar Coronavirus a jihar nan, asibitin ya rufe tare da daina aiki. Bayan tashin ciwonta ne muka garzaya asibitin kashi da ke Dala amma sai suka ki karbarta.

"Muna hanyar neman wani asibitin ne ta cika," yace.

Malam Aminu Ibrahim kuwa ya ce zazzabin cizon sauro da taifot ne ya kashe mahaifinsa.

Ya ce an tabbatar da cewa sune ke damunshi amma sai asibitin Abdullahi Wase suka ki karbarshi. Daga nan ne suka kaishi wani asibitin kudi inda daga baya yace ga garinku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel