Kano: Dandazon jama'a na siyen kayan amfani bayan sassauta doka (Hotuna)

Kano: Dandazon jama'a na siyen kayan amfani bayan sassauta doka (Hotuna)

- A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da sassauta dokar hana zirga-zirga ta jihar don jama'a su yi siyayyar azumin watan Ramadan

- An ga kasuwanni sun yi matukar cika da jama'a inda suke ta hada-hadar siyan abubuwan bukata na amfanin gida

- Amma kuma wani hanzari, farashin kayayyakin bukata ya yi matukar tashi duk da cewa 'yan kasuwar na ajiye da kayan ne ba yanzu suka saro su ba

Kasuwannin jihar Kano sun yi matukar cika a ranar Alhamis bayan gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana zirga-zirga da ta kafa a jihar don jama'a su shiryawa azumin watan Ramadan.

A kasuwar Tarauni inda ake siyar da kayan miya da sauran abubuwa masu lalacewa, an ga jama'a masu tarin yawa suna siyayyar kayan bukata.

Kano: Dandazon jama'a na siyen kayan amfani bayan sassauta doka (Hotuna)

Kano: Dandazon jama'a na siyen kayan amfani bayan sassauta doka (Hotuna)
Source: Twitter

Hakazalika, a kasuwar Dawanau wacce ita ce cibiyar kasuwancin hatsi a Afrika ta yamma, an ga dandazon jama'a na siye da siyar da hatsin don Ramadan da kuma kullen sati biyu da za su fuskanta.

Kamar yadda wani dan kasuwa, Alhaji Danliti Adam yace, an samu kari a farashin kayayyakin abinci a kasuwar tun bayan saka dokar.

Ya ce, duk da sun shirya wa irin wannan al'amarin, amma 'yan kasuwa basu da kayan siyarwa a kasa yanzu.

Kano: Dandazon jama'a na siyen kayan amfani bayan sassauta doka (Hotuna)

Kano: Dandazon jama'a na siyen kayan amfani bayan sassauta doka (Hotuna)
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda marigayi Abba Kyari ya kusan zama mataimakin Obasanjo a 1999 - Mamman Daura

A kasuwar Yankura da ke Yankaba inda ake siyar da kayayyakin lambu, jaridar Daily Trust ta lura cewa an samu tarin mutane ba kamar yadda aka saba ba.

Aminu Ibrahim Yankaba ya ce ya matukar yin mamakin yadda 'yan kasuwa suka hanzarta tada farashin kayayyaki.

Alhaji Muhammad Inuwa ya sanar da jaridar Daily Trust cewa ba shi da zabin da ya wuce ya siya kayayyakin da yake bukata duk da karuwar farashin.

Kano: Dandazon jama'a na siyen kayan amfani bayan sassauta doka (Hotuna)

Kano: Dandazon jama'a na siyen kayan amfani bayan sassauta doka (Hotuna)
Source: Twitter

Ya ce, "Idan ban siya ba yanzu, yaushe nake da tabbacin gwamnatin za ta sassauta dokar? Zai fi kyau in siya abinda zan iya siya yanzu tunda ina bukata.

"Ina da tabbacin cewa babu wanda yake farin cikin halin da muka samu kanmu, amma babu abinda za a iya a kai. Zai fi kyau idan muka sauya tsarin rayuwarmu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel