COVID-19: Ma'aikatan Lafiya bakwai sun kamu da Korona a Borno
– Ma'aikatan Lafiya guda bakwai a jihar Borno sun kamu da kwayar cutar COVID-19
– Kwamishinan Lafiya na jihar, Kwaya-Bura ne ya bayyana hakan a ranar Jumaa a garin Maiduguri
– Kwamishinan ya ce mutum 15 ne suka kamu da cutar a jihar inda biyu cikinsu sun riga mu gidan gaskiya
Kwamishinan Lafiya na jihar Borno, Salihu Kwaya Bura ya ce ma'aikatan lafiya bakwai a jihar sun kamu da kwayar cutar COVID-19 da ake fi sani da coronavirus.
Kwaya-Bura wanda kuma shine sakataren kwamitin kar ta kwana na yaki da annobar Korona a jihar ya bayyana hakan ne a ranar Jumaa a Maiduguri yayin da ya ke bayar da bayani a kan annobar a jihar.
Ya ce mutane 15 ne suka kamu da cutar a jihar kawo yanzu sannan mutum biyu sun mutu.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Kasashe 10 da aka fi samun masu dauke da cutar COVID-19
"An binciko wadanda suka yi cudanya da wandanda suka kamu da cutar kuma ana sa ido a kansu domin ganin halin da suke ciki.
"Mutane sun ankarar da mu game da mutane tara da ake zargin sun kamu, mun yi bincike a kansu, bakwai cikinsu ba su da alamomin cutar amma muna cigaba da bincike a kan biyu," in ji Kwaya-Bura.
Ya jinjinawa al'ummar jihar bisa hakuri da sadaukarwarsu a rana da biyu bayan saka dokar kullen inda ya ce kwamitin kar ka kwanan tana shirin yin sausauci ga dokar don albarkacin watan Ramadana.
Kwaya-Bura ya ce, "Muna son mu ga yadda za mu bari masu sayar da kankara, kosai da shayi da biredi su fara yin sanaarsu a gundumominsu domin mutane su rika saya lokacin shan ruwa."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng