Yan bindiga sun kashe mutane 7 a wani samame da suka kai jahar Kaduna

Yan bindiga sun kashe mutane 7 a wani samame da suka kai jahar Kaduna

Mutane 7 ne suka gamu da ajalinsu a yayin wani hari da gungun miyagu yan bindiga suka kai wasu kauyuka guda uku dake cikin karamar hukumar Chikun na jahar Kaduna.

TheCables ta ruwaito haka zalika mutane 5 sun jikkata a sanadiyyar harin, wanda a yanzu haka suna babban asibitin gwamnati dake unguwar Sabon Tasha don samun kulawa.

KU KARANTA: An samu matsala: Maganin da aka samar don warkar da cutar Corona ya ki aiki a jikin dan Adam

Shugaban kungiyar al’ummar Gbagyi, Peter Aboki ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace tun da tsakar daren Alhamis yan bindigan suka fara hare haren har zuwa karfe 4 na yamma.

Aboki ya bayyana kauyukan da yan bindigan suka kai ma hari kamar haka; Akwunakwo, Kabirasha da kauyen Damba, dukkaninsu a karamar hukumar Chikun.

Yan bindiga sun kashe mutane 7 a wani samame da suka kai jahar Kaduna
Yan bindiga sun kashe mutane 7 a wani samame da suka kai jahar Kaduna
Asali: Facebook

“Sun kashe mutane biyu a Akwunakwo, sun yi awon gaba da wani kurma a Kabirasha, sa’annan sun kashe mutane 5 a Damba, muna zargin duk mutane daya ne suka kai wadannan hare haren.”Inji shi.

Aboki ya kara da cewa yan bindigan sun kona gidaje da ababen hawa da suka tarar a kauyukan, sa’annan sun fasa rumbuna sun kwashe kayan abinci.

“Mun sani cewa gwamnati na iya bakin kokarinta wajen tabbatar da tsaro, amma muna bukatar gwamnati ta kara dagewa saboda ana kashe mutane kuma satar mutane a kullum a yankin nan.

“Jama’a na fargabar shiga yankin nan saboda ayyukan yan bindiga. Shi yasa muke kira ga gwamnati ta dauki duk matakin daya kamata don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.” Inji shi.

A wani labari kuma, jami’an rundunar Yansandan jahar Legas sun samu nasarar kama wani kasurgumin dan fashi da makami daya fitini al’ummar yankin Ikorodu na jahar.

Yansanda sun kama Sanni Abiodun inkiya Abbey Boy ne a wani samame da suka kai wata matattarar yan wiwi dake unguwar Ikorodu ta jahar Legas.

Rahotanni sun ce an kama Abiodun ne a mashayar yan wiwin dake titin Araromi dake Igbogbo, inda Yansandan suka binciko wasu makamai tare da buhunan wiwi a wurin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel