Da dumi dumi: An sallami mutane 10 da suka warke daga cutar Coronavirus a Legas

Da dumi dumi: An sallami mutane 10 da suka warke daga cutar Coronavirus a Legas

An samu karin wasu mutane 10 da suka warke daga annobar cutar Coronavirus a jahar Legas a ranar Juma’a, kuma tuni gwamnatin jahar ta sallame su.

Gwamnan jahar, Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 24 ga watan Afrilu, inda yace mutanen sun hada da maza uku da mata bakwai.

KU KARANTA: Jama’an kasar Makkah sun fuskanci girgizan kasa a daren da aka dauki Azumi

Thecables ta ruwaito gwamnan ya kara da cewa daga cikin wadanda suka rabu da cutar akwai yan kasashen waje guda uku, yan kasar India biyu da dan Philipines 1.

“Duk da samun karin masu kamuwa da cutar, muna farin ciki da nasarorin da muke samu, don haka cutar COVID19 ba mutuwa bace. A yau mun samu mutane 10, maza 3, Mata 7 daga ciki har da yan kasar waje guda 3.” Inji shi.

Da dumi dumi: An sallami mutane 10 da suka warke daga cutar Coronavirus a Legas
Gwamnan Legas
Asali: Twitter

Zuwa yanzu an samu mutane 117 da suka warke daga cutar a jahar Legas, yayin da akwai wasu mutane 582 da suke dauke da cutar a jahar, daga cikin mutane 981 dake da cutar a Najeriya.

A farkon makon nan ne kwamishinan kiwon lafiya na jahar Legas, Akin Abayomi ya bayyana cewa zasu fara bi unguwanni don yi ma jama’a gwajin cutar.

Akin yace hakan ya zama wajibi biyo bayan ganowa da suka yi akwai mutane a cikin unguwannin jahar dake dauke da cutar, kuma suna harbawa iyalai, makwabta da abokansu.

“Muna fatan a cikin mako mai zuwa mu gudanar da gwajin mutane 3000 yayin da muka fara bin unguwannin, amma a sani, idan muka fara gwaji da yawa, zamu samu masu cutar dayawa. Mun sani cewa cutar na yawo a cikin unguwanninmu yanzu haka.” Inji shi.

A wani labari, sakamakon maganin farko da aka fara samarwa da zake tunanin zai warkar da cutar daga jikin masu dauke da ita ya gaza biyan bukata.

Wannan magani mai suna Remdesivir an samar da shi ne a kasar Amurka, kuma an gwada shi a kan wani mai dauke da cutar a kasar China, sai dai bai ya gaza kwarai wajen maganin ta.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO ta tabbatar da gazawar maganin, saboda a cewarta, maganain bai hana kwayar cutar COVID-19 zagaye a cikin jinin mai dauke da cutar ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel