Daga taskar Ramadana: Me ake nufi da daukan Niyyah a ranar farko?

Daga taskar Ramadana: Me ake nufi da daukan Niyyah a ranar farko?

Dukkan godiya sun tabata ga Allah madaukakin Sarki da ya raya mu kuma ya bamu daman shaida wannan wata mai albarka cikin koshin lafiya.

Muna masu rokon Allah ya karbi wannan ibada tamu kuma ya sanyata cikin kyawawan ayyukanmu.

Kamar yadda muka saba a kowace watar Ramadan inda mu kan tunatar da juna kan abubuwa masu muhimmanci tattare da azumi kuma na farko daga cikinsu ita ce Niyyah.

An Niyya

Kudirta Niyyar azumin watar Ramadana wajibi ne kuma yana daya daga cikin sharuddan sihhancin azumin mutum.

Manzon Allah (SAW) yace: "Duk wanda yaki kwanciya da Niyya bashi da azumin." [Nisaa’i 4/196]

Hakan na nufin cewa duk wanda ya samu labarin ganin wata kuma yaki kudirta niyya har Alfjiri ya bayyana bai da azumi a ranar.

Muhallin Niyya na zuci kuma ba furta ta ake yi ba. Furta niyya ya sabawa koyarwan Manzon Allah (SAW) ko da wasu na ganin hakan na da kyau.

Mutum ya tashi yayi Sahur kadai ta isar saboda yana cin abincin ne da niyyar yin azumi.

Niyya a ranar farko ta isa har zuwa karshen watar Ramadan. Amma ya fi falala mutum ya jaddada niyya kullum. [Zaadu-Sa'im shafi na 15]

Menene hukuncin wanda ya wayi gari bai san an ga wata ba sai dai ya samu labari bayan ya yi karin kumallo?

Daliban Sheikh Nasirdeen Albany; Sheikh Salim Al-Hilaaly da Aliy Hasan Ali Abdul Hamid sun kawo cikin littafinsu 'Sifatu Saumun-Nabiy fi Ramadan shafi na 30-33 cewa duk wanda ya waye gari bayan ci ko sha sai ya samu labarin an shiga watar Ramadana, ya kama bakinsa kuma ya cigaba da zumi; hakan ya isar masa, ba sai ya biya ba.

Wajabcin niyya kafin fitowar Alfijir ta sauka daga kansa saboda rashin sani kuma lamarin yafi karfinsa tun da ba gangan yayi ba.

Sun gina fahimtarsu ne bisa Hadisin Ummuna Aisha (RTA) inda tace: "Manzon Allah (SAW) ya bada umurnin azumi ranar Ashura amma yayinda aka wajabta azumin Ramadana, sai ta zama duk wanda ya ga dama yayi, wanda ya ga dama ya ajiye."

Salamata bin Akwa (RTA): "Annabin Allah (SAW) ya umurci wani mutumi daga kabilar Aslam ya sanar da mutane cewa duk wanda yayi karin kumallo ya kama bakinshi na saurar ranar, wand akuma bai ci komai ba ya dau azumi saboda yau take ranar Ashura."

Wannan shine hukuncin azumin Ashura kafin a shafe wajabcin ta. An umurci Sahabbai su kama bakunansu kuma hakan ya isar.

Saboda hakan azumin Ramadana wajibine kuma hukuncin wajabci ba ya canzawa.

Allah ne mafi sani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel