Kano: Sarki Aminu Bayero ya aike da muhimmin sakon Ramadana ga jama'ar jihar
- Tun bayan sanarwar da sarkin Musulmi ya yi na ganin jinjirin watan Ramadana, Sarkin Kano Aminu Bayero ya aika da sako ga jama'ar jihar
- Sarkin ya bukaci jama'ar jihar Kano da su kiyaye dokokin da masana kiwon lafiya da kwararru suka bada na kiyaye kai daga cutar Covid-19
- Sarki Aminu ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta tsananta kokarinta wajen tallafawa mabukata da masu karamin karfi a jihar
Tun bayan sanarwar da sarkin Musulmi ya yi na ganin jinjirin watan Ramadana, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci jama'ar jihar Kano da su kiyaye dokokin da fadar sarkin Musulmi ta fitar na azumin wata mai alfarma.
Ana tsaka da annobar Coronavirus, Sarkin Kano ya bukaci mazauna jihar da su yi amfani da watan wajen addu'a da fatan Ubangiji ya kawo dauki a kan annobar da ta addabi duniya.
"Allah yana ji kuma yana sauraron duk wata bukata da muka mika. Ina kira ga jama'ar jihar Kano da su dinga addu'ar Allah ya kawo karshen annobar nan da ke kunno kai jihar Kano da Najeriya baki daya," Sarkin yace.
Sarki Aminu ya ci gaba da bukatar gwamnati da ta tsananta kokarinta wajen tallafawa mabukata da masu karamin karfi a wannan lokacin.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Yadda marigayi Abba Kyari ya kusan zama mataimakin Obasanjo a 1999 - Mamman Daura
A kokarinsa na wayar da kan jama'ar Kano a kan hatsarin da ke tattare da annobar, Sarkin ya yi kira ga jama'ar da su saurari masana tare da bin dokokin kwararru.
Ya tabbatar wa jama'ar jihar Kano cewa wannan annobar za ta zo karshe kuma nasara ce za ta biyo baya.
"Jama'a ta, na shiga matukar damuwa a kan halin da muke ciki. Ina jin abinda jama'ar jihar Kano ke ji a halin yanzu.
"A don haka dole ne mu kiyaye tsaftace kanmu, kiyaye shawarwarin kwararru da kuma addu'a. Ubangiji ya tsaremu tare da kawo mana dauki," Sarkin ya tabbatar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng