An kama mutumin da ya haike wa matarsa har ta mutu a Jigawa

An kama mutumin da ya haike wa matarsa har ta mutu a Jigawa

Rundunar yan sanda na jihar Jigawa ta kama wani mutum da aka zargin ya yi matarsa fyade har sai da ta mutu a kauyen Kankaleru da ke karamar hukumar Ringim na jihar.

A sanarwar da ya fitar a ranar Jumaa, Mai magana da yawun rundunar a jihar, Abdu Jinjiri ya tabbatar wa Channels Television kama mutumin.

A cewar Jinjiri, wanda ake zargin, Alasan Audu ya aikata laifin ne bayan ta ki amincewa su yi kwanciya ta aure.

Jigawa: An kama magidancin da ya yi wa matarsa fyade har sai da ta mutu

Jigawa: An kama magidancin da ya yi wa matarsa fyade har sai da ta mutu
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kasashe 10 da aka fi samun masu dauke da cutar COVID-19

Kakakin yan sandan ya yi bayanin cewa an tilastawa matashiyar mai shekaru 17 auren mutumin ne mai shekaru 3O.

Lamarin ya faru ne kwanaki 2O bayan daura musu aure.

Wani sashi na sanarwar ta ce, "Bincike ya nuna cewa misalin karfe 4 na asuba, wanda ake zargin ya kusanci (marigayiyar) a matsayinsa na mijin ta amma ta ki amincewa ya biya bukatarsa tunda dama ba shi ta ke son a aura mata ba da farko.

"Ana zargin a hakan ne ya yi amfani da karfi da yaji ya biya bukatarsa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel