Yanzu-yanzu: Mahaifiyar ministan Ilimi, Adamu Adamu ta rasu

Yanzu-yanzu: Mahaifiyar ministan Ilimi, Adamu Adamu ta rasu

Allah ya yi wa Fatima Adamu, mahaifiyar ministan Ilimi na Najeriya, Adamu Adamu rasuwa.

Ta rasu ne a safiyar ranar Jumaa kamar yadda premium Times ta ruwaito.

Sanarwar da mai magana da yawun maaiakatar Ilimi, Ben Gooong ya fitar ta ce Mr Adamu ya tabbatar da cewa mahaifiyarsa ta rasu a safiyar ranar Jumaa.

Mr Gooong ya ce a halin yanzu ana gudanar da janaizar ta a garin Azare da ke Bauchi bisa tsarin koyarwar addinin musulunci.

Yanzu-yanzu: Mahaifiyar ministan Ilimi, Adamu Adamu ta rasu
Yanzu-yanzu: Mahaifiyar ministan Ilimi, Adamu Adamu ta rasu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kasashe 10 da aka fi samun masu dauke da cutar COVID-19

Mr Gooong ya ce, "Sauran bayanai za su iso nan gaba."

Shugaba Muhammadu Buhari ya fara nada Mr Adamu a matsayin minista ne a ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2015 tare da wasu ministocin 35 yayin da shugaban ya yi nadinsa na farko.

Har wa yau, Shugaban kasar ya sake nada shi ministan a ranar 21 ga watan Augustan 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164