Yanzu-yanzu: NJC ta dakatar da alkalai biyu saboda wasu laifuka

Yanzu-yanzu: NJC ta dakatar da alkalai biyu saboda wasu laifuka

Majalisar Koli ta Alkalan Najeriya, NJC, ta dakatar da alkalai biyu tare da bayar da shawarar yi musu ritayar dole na dindinin bayan samunsu da saba dokokin aiki.

Daya daga cikin alkalan ya yi karya ne yayin bayar da shekarunsa shi kuma na biyun ya ki yanke hukunci cikin lokacin da aka bashi a cewar NJC ta bakin Kakakinta, Soji Oye a ranar Jumaa.

Ana jiran shugaban kasa ya amince da shawarar yi musu murabus a halin yanzu kamar yadda remium Times ta ruwaito.

Kazalika, NJC din ta kuma wanke wasu alkalai daga tuhumar da ake musu kana ta amince da nadin sabbin alkalai 7O.

Majalisar ta kuma kafa kwamiti na musamman da za ta bayar da shawarwarin yadda kotuna za su cigaba da yin sharia duk da dokar kulle da aka saka a jihohi sakamakon annobar Covid-19.

DUBA WANNAN: Kasashe 10 da aka fi samun masu dauke da cutar COVID-19

Wani sashi daga sanarwar ya ce:

"Majalisar Koli ta Alkalai karkashin jagorancin Babban Alkalin Kasa, Dr. Justice I.T. Muhammad, CFR, a taron ta na karo 91 da aka gudanar ta yanar gizo a ranar 22 da 23 ga watan Afrilun 2020, ta kafa kwamitin mutum 1O da za su bayar da sharwarin yadda kotuna za su cigaba da aiki duk da dokar kulle da Covid-19 ta janyo."

An bawa kwamitin kwabaki 14 ta kammala aikin ta.

"Kwamitin ta kuma bayar da shawarar yi wa Hon. Justice Francis Chukuwa Abosi, shugaban riko, na kotun Customary na daukaka kara da ke Imo da Hon. Justice Aliyu Musa Liman na babban Kotun jihar Bauchi murabus din dole nan take.

"An bayar da shawarar yi wa Hon. Justice Francis Chukuwa Abosi riyatar dole ne saboda canja shekarar haihuwarsa da ya yi daga 1950 to 1958."

Hakan na nufin ya dace ya yi ritaya a Nuwamban 2015 lokacin ya cika shekaru 65 kamar yadda dokar aikin gwamnati ta tanda.

"An bukaci gwamnan Bauchi ya yi wa Hon. Justice Aliyu Musa Liman murabus din dole domin bincike ya nuna cewa ya ki yanke hukunci a kan kara mai lamba BA/100/2010, tsakanin Abubakar Isa da Sheik Tahir Usman Bauchi cikin watanni uku kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 ta tanada."

Majalisar na ganin saba doka ne yadda ya shariar kusan tsawon shekaru hudu wanda ya saba wa sashi na 292 (1) (b) na kundin tsarin Najeriya ta 1999.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel