Rundunar Sojin saman Najeriya ta kara inganta ayyukan gudanarwa na dakarunta

Rundunar Sojin saman Najeriya ta kara inganta ayyukan gudanarwa na dakarunta

- Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta horar da wasu kwararrun ma'aikatan lafiyarta a kan ingantacciyar hanyar jinya da kuma kwashe wadanda suka ji rauni a filin yaki

- An horar da ma'aikatan ne kan yadda zasu tseratar da rayuwar dakaru da suka ji rauni a filin daga

- Hukumar sojin ta ce horon na tsawon mako daya wata gaba ce cikin manufofinta na inganta ayyukan dakarunta

A kokari da take yi na kara karfin gwiwar dakarunta, rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kammala horas da wasu kwararrun ma'aikatan lafiyarta a kan ingantacciyar hanyar jinya.

Rundunar sojin ta sanar da cewa ta horar da ma'aikatan ne a kan nagartacciyar hanyar tseratar da rayuwar dakarun da suka ji rauni tare da kwashe su daga filin daga.

Jami'in hulda da al'umma na rundunar sojin, Air Commodore Ibikunle Daramola, shi ne ya bayar da wannan sanarwa a ranar Laraba, 23 ga watan Afrilun 2020.

An gudanar da horon na tsawon mako daya a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Nnamdi Azikwe da ke garin Abuja.

Hukumar sojin ta ce manufar wannan horo ita ce bunkasa ayyuka tare da kara wa jami'anta kaifi wajen gudanar da ayyukansu cikin inganci.

KARANTA KUMA: Dalilan da suka sanya cutar Coronavirus ta ke ci gaba da yaduwa a Kano

Ma'aikatan rundunar sojin da aka horas sun samu kwarewa a kan aikin jinya da kuma gaggawar kwashe dakarun da suka ji rauni a filin yaki da mika su cibiyar duban lafiya ta kurkusa.

Da yake jawabi a karshen lamarin, shugaban hafsin sojin sama na Najeriya, Air Vice Marshal Sadique Abubakar, ya yi amanna da nuna gamsuwarsa a kan yanayin horon.

Shugaban hafsin sojin yana mai cewa, a tsawon shekaru hudu da rabi da suka gabata, hukumar ta yi kokarin bunkasa harkokin gudanarwar dakarunta musamman a bangaren kula da lafiyarsu.

Ya ci gaba da cewa, tabbatar da lafiyar ma'aikatansa bata takaita kadai a kan dakaru da iyalansu ba, har da ma tabbatar da samun ingatacciyar kulawa yayin da suka samu rauni a filin yaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel