Coronavirus: Gwamnan Bauchi ya rufe masallatan Juma’a, ya hana taron tafsiri

Coronavirus: Gwamnan Bauchi ya rufe masallatan Juma’a, ya hana taron tafsiri

Gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad ya sanar da umarnin garkame wuraren bauta, wuraren taron jama’a da kuma kasuwanni a kokarinsa na dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ma al’ummar jahar jawabi a ranar Alhamis, inda yace ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

KU KARANTA: Corona: Kotun tafi da gidanka ta kama mutane 500 da laifin karya dokar ta baci a Abuja

Gwamnan yace sun tattauna matsalar yaduwar cutar a Bauchi, da sauran matsalolin kiwon lafiya da suka dabaibaye al’ummar jahar.

A yanzu akwai mutane 8 dake dauke da cutar a jahar.

Gwamnan ya kara da cewa sun dakatar da duk wani gangamin sauraron tafsirin Al-Qur’ani a watan azumin Ramadana, sai dai ga mai karatu da mai fassara kadai.

Coronavirus: Gwamnan Bauchi ya rufe masallatan Juma’a, ya hana taron tafsiri

Coronavirus: Gwamnan Bauchi ya rufe masallatan Juma’a, ya hana taron tafsiri
Source: Twitter

“Mun yi haka ne don rage cakuduwar jama’a a irin wannan wuri sakamakon hakan zai kara yaduwar cutar a tsakanin al’umma ta hanyar mu’amala, don haka gwamnati ta yanke hukuncin daukan nauyin tafsirai a gidajen rediyo da talabijin don jama’a su saurara daga gida.

“Gwamnatinmu ta dakatar da sallar Juma’a da kuma bauta a coci-coi, taron daurin aure, bukukuwa, zaman makoki da ta’aziyya, gidajen rawa, wuraren motsa jiki da duk wasu tarukan zumunta.

“Kasuwanninmu za su dinga aiki a ranakun Litinin, Laraba da Asabar, daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana daga ranar 26 ga watan Afrilu. Haka zalika mun hana aikin Acaba da na Keke Napep.” Inji shi.

Gwamnan ya ja kunnen Musulmai da cewa kada su ga don an shiga watan Ramadan su yi sakaci da dokar kare yaduwar annobar, don haka yace ya dakatar da asham, tahajjud da I’itikaf.

“Ina kira ga jama’a su gudanar da sallolinsu a gidajensu, ko a haka ma, don Allah ku tabbata kuna tsaya nesa nesa da juna, a yanzu dai mun bari a gudanar da sallolin farilla 5 a cikin jam’i, amma a Masallatan unguwanni.

“Kada a wuce mintuna 10 wajen gudanar da wadannan salloli, kuma da zarar an idar kowa ya kama gaban sa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel