Covid-19: Buhari ya halarci taron ECOWAS ta yanar gizo (Hotuna)

Covid-19: Buhari ya halarci taron ECOWAS ta yanar gizo (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci taron gamayyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma a Abuja da aka yi a ranar Alhamis.

Taron an yi shi ne ta bidiyon hadi tsakaninsa da shugabannin kasashen Afrika ta yamma.

Sun samu tattaunawa ne a kan illar annobar Coronavirus a yankin.

A yayin taron, shugabannin kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta yamma an nada shi a matsayin gwarzon yaki da cutar coronavirus a yankin.

Covid-19: Buhari ya halarci taron ECOWAS ta yanar gizo (Hotuna)

Covid-19: Buhari ya halarci taron ECOWAS ta yanar gizo (Hotuna)
Source: Twitter

Shugabannin kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) sun nada shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, a matsayin gwarzon da zai jagoranci yaki da annobar cutar covid-19 a yankin.

KU KARANTA: COVID-19: Mun garzaya jihar Kano domin kada ta zamo cibiyar cutar - FG

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ne ya sanar da nadin da aka yi wa Buhari a sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta (tuwita).

Covid-19: Buhari ya halarci taron ECOWAS ta yanar gizo (Hotuna)

Covid-19: Buhari ya halarci taron ECOWAS ta yanar gizo (Hotuna)
Source: Twitter

ECOWAS ta gudanar da taron ne domin tattaunawa a kan kokarin dakile yaduwar annobar covid-19 a kasashen da ke zaman mamba a kungiyar.

A cikin wata sanarwa da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fitar ranar Talata, ta bayyana cewa akwai kimanin mutum 5,774 da aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar covid-19 a yankin Afrika ta yamma.

Daga cikin adadin mutanen, mutum 1,616 sun warke, yayin da mutum 147 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon kamuwa da kwayar cutar covid-19.

Covid-19: Buhari ya halarci taron ECOWAS ta yanar gizo (Hotuna)

Covid-19: Buhari ya halarci taron ECOWAS ta yanar gizo (Hotuna)
Source: Twitter

Ko a makon jiya, sai da kungiyar hadakar kasashen nahiyar Turai (EU) ta bawa Najeriya tallafin Yuro miliyan hamsin (£50m) domin yaki da annobar cutar covid-19.

Shugaban tawagar wakilan EU, Ambasada Ketil Karlsen, ne ya sanar da hakan yayin ziyarar da suka kai wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa ranar Talata, 14 ga watan Afrilu.

Yayin ziyarar, tawagar wakilan ta mika sakon jinjinar EU ga shugaba Buhari a kan kokarin da gwamnatin Najeriya ta ke yi na yaki da annobar covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel