Kallo ya koma sama: Jami’an rundunar Yansanda sun dambace da juna a jahar Edo

Kallo ya koma sama: Jami’an rundunar Yansanda sun dambace da juna a jahar Edo

Bidiyon wasu jami’an rundunar Yansandan Najeriya ya bayyana a shafukan sadarwar zamani yayin da suke baiwa hammata iska babu kakkautawa.

Rahotanni sun bayyana wannan lamari ya faru ne a jahar Edo, sai dai ba’a bayyana takamaimen abin da ya hadasu fadan ba.

KU KARANTA: Sakamakon bincike: An bankado dabbar da ta yi sanadiyyar samuwar Coronavirus a duniya

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Twitter, @ParodySpokesman ne ya janyo hankalin rundunar Yansanda ga wannan bidiyon abin kunya bayan ya wallafa bidiyon a shafinsa.

A cewarsa: “Ina da yakinin shugabancin rundunar Yansanda a karkashin babban sufeta IGP Adamu ba zasu kauda kai daga wannan lamari ba, mu cigaba ga bada rahoton duk wani jami’in dansanda da ke aikata laifi don bayar da gudunmuwar garambawul da ake yi a rundunar Yansanda.”

Sai dai jin kadan rundunar Yansandan Najeriya ta mayar da martani game da bidiyon tare da amsa ma @ParodySpokesman, ta shafinta na kafar sadarwar zamani na Twitter, inda tace:

“Yansandan guda biyu sun hada Kofur Ozimende Aidonojie mai lamba F/NO 41112 da Kwanstebul Salubi Stepehen mai lamba F/NO 516384, a yanzu haka an kama su, an daure su. Kuma suna fuskantar matakin ladabtarwa a babban ofishin Yansandan jahar Edo.

“Rundunar na sanar da jama’a cewa wannan abin kunyar da suka tafka ba halin ta bane, kuma ba za ta lamunci hakan ba, za mu sanar da jama’a sakamakon binciken da muka gudanar a kansu da kuma hukuncin da muka yanke musu.

“Muna fata hakan zai kare sake aukuwar kwatankwacin wannan rashin da’a a gaba, kuma muna tabbatar ma jama’a cewa za mu yi adalci a cikin wannan lamari.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel