COVID-19: Gwamnatin tarayya da kungiyar Kwadago sunyi taro a kan dokar hana fita

COVID-19: Gwamnatin tarayya da kungiyar Kwadago sunyi taro a kan dokar hana fita

Gwamnatin Tarayya ta ce kada mutane su tayar da hankulan su da hankulan game da fargabar da ake yi na yiwuwar Kungiyar Kwadaga na Kasa, NLC, za ta dauki mataki a kan dokar hana fita da gwamnati ta saka a jihohi saboda COVID-19.

Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa a kan COVID-19, Boss Mustapha ne ya bayanna hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin jawabin kwamitin karo na 18.

A cewarsa, Kungiyar Kwadagon ba ta taba yin wannan barazanar ba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

COVID-19: Gwamnatin tarayya da kungiyar Kwadago sunyi taro a kan dokar hana fita

COVID-19: Gwamnatin tarayya da kungiyar Kwadago sunyi taro a kan dokar hana fita
Source: Twitter

Shugaban NLC, Comrade Ayuba Waba ya rubuta wa shugaba Muhammadu Buhari wasika inda ya gargadin cewa akwai yiwuwar afkuwar tashin hankula idan aka tsawaita dokar hana fita domin halin da maaikata ke ciki.

DUBA WANNAN Covid-19: Aisha Buhari ta jinjinawa matan tsoffin shugabannin kasa a kan gudumawa

Amma Mustapha ya ce gwamnatin tana cigaba da yaki da cutar ta Korona a kasar kuma tana tuntubar kungiyar ta NLC lokaci zuwa lokaci.

Ya kara da cewa ya gana da Waba a ranar Alhamis a Abuja, kuma shugaban kungiyar Kwadagon ya bashi shawarwari a kan yadda za a cigaba da dakile yaduwar cutar a kasar.

Ya ce, "Ina tsamannin yana tuntubar mutane kuma yana sauraran ma'aikatansa kuma yana lura da yadda sauran kasashe ku rayuwa sakamakon dokar hana fita.

"Wasu da cutar ya fara sauki a kasashensu sun fara sassauta dokar kuma sun fara bude maaikatu a kasashen su.

"Saboda haka babu wata barazana daga kungiyar kwadago, muna tuntubar su. Suna da ra'ayayinsu kuma suna tattaunawa da mu game da matakan da suke dauka domin tabbatar da cewa munyi aiki tare."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel