Yanzu-yanzu: An ga wata, a tashi gobe Juma'a da azumi - Sarkin Musulmi

Yanzu-yanzu: An ga wata, a tashi gobe Juma'a da azumi - Sarkin Musulmi

Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na biyu, ya sanar da ganin watar Ramadana mai albarka a yau Alhamis, 29 ga watan Sha'aban 1441AH wanda yayi daidai da 23 ga watan Afrilu 2020.

Ya umurci al'ummar Musulman Najeriya su dau azumi gobe 1 ga watan Ramadana 1441AH wanda yayi daidai da 24 ga Afrilu, 2020.

Yace: "A yau 24 ga Afrilu 2020 ya zama ranar farkon watar Ramadan 1441 bayan Hijra Insha Allah. Saboda haka muna kira ga dukkan Musulmai maza da mata su dau azumi."

Kalli bidiyon:

Gabanin sanarwan Sarkin Musulmi, Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da al'ummar kasar ganin jinjirin watan Ramadana mai alfarma yau Alhamis, 23 ga Afrilu 2020, jaridar Al-Ekhbariya ta ruwaito.

Saboda haka, ranar Juma'a, 24 ga watan Afrilu zata zama ranar farkon watan Ramadana 1441AH kuma ranar fara azumin bana a Saudiyya.

Hakazalika sauran kasashen Larabawa irinsu Kuwait, Qatar, Tunusiya, Lebanon, Misra, Dubai UAE da Iraqi.

Amma Sarkin Oman ya bayyana cewa basu ga watan ba kuma saboda haka sai ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel