Covid-19: Aisha Buhari ta jinjinawa matan tsoffin shugabannin kasa a kan gudumawa

Covid-19: Aisha Buhari ta jinjinawa matan tsoffin shugabannin kasa a kan gudumawa

A ranar Alhamis uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta wallafa sakon godiya da fatan alheri a shafukanta na sada zumuntar zamani.

Aisha Buhari ta mika godiyarta ga matan tsoffin shugabannin kasa da irin tallafin da suka bada don yakar annobar Covid-19 a kasar nan, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ta mika godiyarta ga matan tsoffin shugabannin kasa da suka hada da Patience Jonathan da ta bada cibiyar killacewa, magunguna da kuma kayan kariya ga ma'aikatan lafiya.

Ta kara da cewa za a yi amfani da kayayyakin yadda ya dace kuma za a raba su zuwa inda ya dace.

"Ina son mika godiyata ga wadanda suka amsa kiranmu don taimakawa wajen yaki da cutar Covid-19.

"Ina godiya ga 'yan Najeriya ballantana matan tsoffin shugabannin kasa a kan sakonnin alherin da kuma gudumawa da suka bada.

"Ina godiya ga Dame Patience Jonathan da ta bada otal dinta wanda yake kotu a kan a yi cibiyar killacewa da shi na wucin-gadi.

"Duk kayayyakin da aka bada da suka hada da gadajen asibiti, zannuwan gado, kayayyakin kariya da kuma magunguna, za a raba su da gaggawa," ta ce.

Covid-19: Aisha Buhari ta jinjinawa matan tsoffin shugabannin kasa a kan gudumawa
Covid-19: Aisha Buhari ta jinjinawa matan tsoffin shugabannin kasa a kan gudumawa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Covid-19: Korona ta kashe mutum biyu a Borno da Ribas, mutum 6 sun sake kamuwa

A wani labari na daban, kungiyar likitoci da ke aiki da jihar Legas ta bayyana cewa likitoci 3 ne na kungiyar suka kamu da cutar coronavirus a jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Dr Oluwajimi Sodipo da sakataren kungiyar, Dr Ismail Ajibonwo ne suka sanar da hakan a ranar Alhamis a shafin kungiyar na Instagram.

Sodipo da Ajibonwo sun ce likitocin uku suna cibiyar killacewa ta jihar da ke Legas don karbar magani.

Sun ce a halin yanzu dai rashin lafiyar likitocin bai tsananta ba kuma suna samun goyon baya daga kungiyar.

Shugabannin kungiyar sun shaida cewa likitocin na aiki ne babban asibitin Alimosho, asibitin Ikorodu da kuma asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel