Yanzu-yanzu: An ga jinjirin watan Ramadana a kasar Saudiyya

Yanzu-yanzu: An ga jinjirin watan Ramadana a kasar Saudiyya

Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da al'ummar kasar ganin jinjirin watan Ramadana mai alfarma yau Alhamis, 23 ga Afrilu 2020, jaridar Al-Ekhbariya ta ruwaito.

Saboda haka, ranar Juma'a, 24 ga watan Afrilu zata zama ranar farkon watan Ramadana 1441AH kuma ranar fara azumin bana a Saudiyya.

Yanzu-yanzu: An ga jinjirin watan Ramadana a kasar Saudiyya

Yanzu-yanzu: An ga jinjirin watan Ramadana a kasar Saudiyya
Source: UGC

KU KARANTA: Ma'aikatan asibiti 40 suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya

A nan gida kuwa, Mai alfarma sarkin Musulmi, Sulta Sa'ad Abubakar, ya yi kira ga al'ummar Musulmi su nemi jinjirin watan Ramadana a yau Alhamis.

Ya bayyana cewa idan an gani, to za'a sanar da gobe Juma'a matsayin ranar 1 ga watan Ramadada. Amma idan ba'a gani ba, za'a dau azumi ranar Asabar.

Jama’tul Nasril Islam JNI ta yi kira ga kafatanin Musulman Najeriya da su saurari sanarwar mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar kafin su dauki azumin watan Ramadan.

Sakataren JNI, Dakta Khalid Aliyu ne ya yi wannan kira cikin wata sanarwa da ya fitar, inda yace Sarkin Musulmi ne kadai ke da hakkin sanar da ganin watan Ramadan.

Don haka Khalid ya nemi Musulmai su nemi wata, sa’annan su sanar da shuwagabannin addinin Musulunci mafi kusa domin a sanar da Sarkin kafin a sanar ma al’umma.

Mai alfarma Sarkin Musulmai zai sanar da ganin watan bayan gudanar da bincike an tabbatar da sakon da aka aika masa na ganin watan gaskiya ne, daga nan sai ya sanar ma jama’a.

Hakazalika, sanarwar ta nemi Musulmai su gudanar da dukkanin ibada na watan Ramadana a gida, har da sallar Tarawihi bisa umarnin gwamnati na kulle masallatai saboda Coronavirus.

Haka zalika ba za’a gudanar da tafsiri a Masallatai ba duk saboda wannan umarni na gwamnati, an yi hakan ne don kare yaduwar cutar annobar Coronavirus a cikin al’umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel