Covid-19: 'Yan sanda sun halaka wani mutum da ya yi yunkurin daukarsu bidiyo suna kwallo

Covid-19: 'Yan sanda sun halaka wani mutum da ya yi yunkurin daukarsu bidiyo suna kwallo

- 'Yan sanda biyu a kasar Mozambique sun shiga hannun hukuma bayan sun yi wa wani mutum dukan da suka kai shi har lahira

- Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Abdulrazak mai shekaru 44 ya tunkari 'yan sandan ne don sanar dasu cewa suna take dokar nisantar juna

- Bayan sun kammala kora matasa gida, 'yan sandan sun dage don yin wasan kwallon kafa a filin amma sai mutumin ya yi barazanar daukarsu bidiyo

'Yan sanda biyu ne a kasar Mozambique sun yi wa wani mutum dukan mutuwa bayan ya yi barazanar yi musu bidiyo bayan ya gansu suna wasan kwallon kafa duk da dokar hana zirga-zirga da kasar ta saka.

Kamar yadda Premium Times ta wallafa, wanda aka kashe din mai suna Abdulrazak na da shekaru 44 a duniya.

Ya tunkari jami'an 'yan sandan ne a ranar Lahadi a yankin Munhava na Beira, daya daga cikin manyan biranen kasar.

Razak ya sanar da 'yan sandan cewa suna karya dokar nisantar juna da gwamnati ta gindaya don gujewa yaduwar muguwar cutar coronavirus.

Kamar yadda wani gidan talabijin na kasar ya bayyana, wadannan 'yan sandan ne ke kora matasa idan suka ga sun yi dandazo don wasan kwallon kafa.

Rahotanni sun bayyana cewa, hukuma ta damke 'yan sandan kuma za su fuskanci bincike kafin hukuncin da ya dace hya biyo baya.

Covid-19: 'Yan sanda sun halaka wani mutum da ya yi yunkurin daukarsu bidiyo suna kwallo
Covid-19: 'Yan sanda sun halaka wani mutum da ya yi yunkurin daukarsu bidiyo suna kwallo
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda za a shawo kan matsin rayuwa a Najeriya - Atiku

Hukumar 'yan sandan ta yi alkawarin daukar dawainiyar iyalan mamacin.

Mozambique kasa ce mai a kalla mutum miliyan 29. A halin yanzu kasar tana da mutum 41 da aka tabbatar suna dauke da cutar coronavirus.

Ta fara samun mai cutar a kasar ne a ranar 22 ga watan Maris. Mutumin dan shekaru 75 ya dawo daga Ingila ne inda ya kwaso cutar.

Kasar ta dakatar da tashi da saukar jiragen sama. Ta rufe iyakokinta tare da saka dokar ta-baci a kasar don tsayar da yaduwar cutar.

Duk da wannan tsauraran dokokin da kasar ta dauka na hana yaduwar kwayar cutar, an samu jami'an tsaro da suka karyata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel