China ta bai wa Najeriya tallafin N48m na yakar cutar Coronavirus

China ta bai wa Najeriya tallafin N48m na yakar cutar Coronavirus

- Gwamnatin China ta bai wa Najeriya gudunmuwar Naira miliyan 48 a yunkurin ta tallafawar kasa domin yakar annobar cutar coronavirus

- Jakadan kasar China, Zhou Pingjian, ya ce gudunmuwar wani tabbaci ne na amincin da ke tsakanin kasashen biyu

- Gwamnatin China ta ce a shirye ta ke tsaf wajen goyon bayan Najeriya a yayin da ta ke yakar annobar Coronavirus

A ci gaba da fafutikar dakile yaduwar annobar cutar Coronavirus, gwamnatin kasar China ta bai wa Najeriya gudunmuwar zunzurutun kudi na kimanin N48,120,000.

Jakadan kasar China a Najeriya, Zhou Pingjian, shi ne ya gabatar da takardar banki mai dauke da shaidar wannan zunzurutun kudi zuwa ga kwamiti yakin da cutar corona na Najeriya.

Kamar yadda rahotanni daga kamfanin talbijin na Channels TV suka bayyana, Mista Pingjian ya gabatar da shaidar kudin ne cikin birnin Abuja a ranar Alhamis.

Da ya ke gabatar da jawabai, Jakadan ya ce wannan gudunmuwa karin tabbaci ne na aminci da kuma dadaddiyar zumunta da ke tsakanin kasashen biyu.

Takadar banki mai dauke da shaidar gudunmuwar da China ta bai wa Najeriya

Takadar banki mai dauke da shaidar gudunmuwar da China ta bai wa Najeriya
Source: Twitter

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin China a shirye ta ke tsaf wajen ci gaba da goyon bayan Najeriya a yayin da ta ke yakar annobar Coronavirus.

KARANTA KUMA: Ganduje ya sake sabunta nadin mukamin shugaban hukumar yaki da rashawa na Kano

Ya ke cewa, "kasar China ba za ta taba barin aminanta ba cikin halin hau'la'i, kuma taimakon da ta ke bayarwa ba ya da wani hadi da son zuciya ko son kai."

"Ba don dokar kulle na hana shige da fice da gwamnati ta shimfida ba, kasar China ba za ta gushe ba wajen ci gaba da goyon bayan Najeriya kuma a shirye ta ke tsaf wajen ba ta duk wani taimako iyaka karfinta a yayin da bukatar hakan ta taso."

"Muna da cikakken kwarin gwiwa kan kudirin da Najeriya ta sanya gaba na ganin bayan annobar coronavirus."

"Muna kuma da yakinin cewa Najeriya za ta ci gaba da daukar mutanen China a matsayin 'yan kasarta."

Babban jigo na kwamitin yaki da cutar corona a Najeriya, Dr. Sani Aliyu, ya yabawa Mista Zhou dangane da wannan gudunmuwa, da cewa Najeriya ba za ta taba mance ire-iren taimakon da ta ke samu daga kasar China ba.

Ana iya tuna cewa, a ranar 8 ga Afrilun 2020, gwamnatin Najeriya tayi maraba da tawagar wasu kwararrun likitoci 15 daga kasar China da za su taimakawa kasar nan yakar cutar corona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel