COVID-19: Tambuwal ya bullo da sabuwar tsarin ciyarwa a watan Ramadan

COVID-19: Tambuwal ya bullo da sabuwar tsarin ciyarwa a watan Ramadan

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya kafa kwamiti mai mambobi 32 wadda za su raba wa alumma abinci lokacin azumin watan Ramadan ta hanyar bin dokokin kiyaye yaduwar COVID-19.

Sanarwar ta Tambuwal ya fitar ta bakin Kakakinsa, Muhammad Bello ya ce wannan tsarin ciyarwar yana da banbanci da irin wanda aka yi a shekarun baya kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamnan ya ce masu rabon abincin za su bi dokokin da Cibiyar Lafiya ta Duniya, WHO, ta gindaya domin kare yaduwar cutar COVID-19 a tsakanin alumma.

COVID-19:Tambuwal ya bullo da sabuwar tsarin ciyarwa yayin Ramadan
COVID-19:Tambuwal ya bullo da sabuwar tsarin ciyarwa yayin Ramadan
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda za a shawo kan matsin rayuwa a Najeriya - Atiku

Ya yi bayani cewa, "Mun yi hakan ne don bin dokoki, za a raba wa wasu danyen abinci yayin da wasu wuraren kuma za a raba wa mutane dafafen abinci."

Gwamnan ya kara da cewa adadin kudin da aka ware domin ciyarwar ya karu daga Naira miliyan 380 a bara zuwa N500 a bana saboda adadin masu bukata ya karu kuma farashin kayan abinci ya sauya.

Tambuwal ya ce sakataren gwamnatin jihar, Saidu Umar ne zai jagoranci kwamitin yayin da dan majalisar tarayya mai wakiltan Silame/Binji, Mani Maishinku zai kasance cikin mambobin.

Mambobin sun hada da Abubakar Shamaki, Abdullahi Maigwandu, Bello Aliyu, Abubakar Jibril, Malam Abubakar Mabera, Auwal Romo, Lawal Maidoki, Prof. Abubakar Yagawal, Bello Yabo da Yahaya Na Malam Boyi.

Akwai kuma Prof. Mansur Ibrahim, Malam Amadu Helele, Malam Nura Hausare, Dr Jabir Sani-Maihula, Malam Zaruku Masallacin Shehu, Malam Husaini Gandu, Ibrahim No Delay, Farouk Suyudi da Bello Guiwa.

Sauran mambobin su ne arkin Yakin Gagi, Ubandoman Sabon Birni, Sarkin Kudun Guiwa, Prof. Sadiya Bello, Malama Aishatu Salihu, Malama Zainab Binji, Hajiya Inno Attahiru da Hajiya Fati Illo.

Gwamnan ya ce, "Maaikatar Lafiya da hukumomin tsaro na jihar za su samu wakilai daya kowannensu a kwamitin.

"Tsohon sakatare a maaikatar harkokin addini, Alhaji Bello Mailato shima zai yi aiki a matsayin sakatare a kwamitin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel