Jiragen yakin NAF sun yi ruwan wuta a mafakar yan Boko Haram a Borno – Hedkwatan Tsaro

Jiragen yakin NAF sun yi ruwan wuta a mafakar yan Boko Haram a Borno – Hedkwatan Tsaro

– Sojojin Saman Najeriya sun sake yi wa yan Boko Haram ruwan wuta a wani mafakarsu da ke dajin Sambisa

– Rundunar sojin ta yi amfani da masu leken asiri da kuma naurorin zamani na leken asiri inda ta tabbatar yan taadan na gidan kafin ta kai hari

– Dakarun na NAF sun yi nasarar lalata gidan tare da kashe yan Boko Haram da dama ciki har da wadanda suka yi yunkurin mayar wa jirgin yakin martani

Hedkwatan Tsaro ta Najeriya ta ce Dakarun Sojojin Saman ta karkashin Operation Lafiya Dole (OPLD), sun lalata wani gida da yan taaddan Boko Haram ke zaune a Bulawa kusa da dajin Sambisa a jihar Borno.

Mai kula da sashin watsa labarai na hedkwatan tsaron, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana hakan cikin wata sako da ya fitar a shafin Twitter a ranar Alhamis a Abuja.

DUBA WANNAN: Kano: Ganduje ya yi magana a kan dage dokar hana zirga-zirga

Enenche ya ce sojojin sun kai harin ne a ranar 21 ga watan Afrilu bayan samun bayanan sirri daga masu leken asiri da kuma amfani da naurar leken asiri ta zamani inda suka tabbatar yan taadan na gidan.

Ya yi bayanin cewa an yi amfani da jiragen yaki da Rundunar Sojin Saman Najeriya inda suka yi ruwan bama bamai a gidan suka kashe yan taadan tare da lalata gidan.

A cewarsa, an kashe wasu daga cikin yan taadan da ke zaune a gidan yayin harin.

Ya ce, "An murkushe wasu daga cikin yan Boko Haram din da su kayi yunkurin neman mafaka domin su kai wa jirgin yakin NAF hari bayan tarwatsa gidan.

"Rundunar Sojojin Najeriya za ta cigaba da jajiracewa wurin aikin da ta sa a gaba na samar da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso Gabas da kare Najeriya daga makiyan ta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel